Anambra
Oluremi Tinubu za ta ziyarci Anambra ranar 10 ga Satumba, inda za ta tallafa wa mutane 5,000 tare da ƙaddamar da shirin Bankin Abinci na Al’umma a Kudu maso Gabas.
NDC ta yi watsi da jerin sunayen 'yan takarar jihar Anambra da INEC ta wallafa, tana mai zargin cewa an shigar da su ne ta bayan fage ba tare da amincewarta ba.
Shugabannin al’ummar Arewa da ke zaune a jihar Anambra sun karyata zargin cewa Peter Obi ya nuna musu wariya ko ya rushe masallaci a lokacin mulkinsa.
Kalaman Peter Gregory Obi cewa ya kai ziyara dukkan makarantun sakandaren Anambra sun jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu suka goyi bayansa.
Ozonna Soludo, dan gwamnan jihar Anambra ya jawo takaddama a kafafen sada zumunta bayan ya saki bidiyon wakar sukar manyan mutane har da mahaifinsa.
Peter Obi ya bayyana cewa a shirye yake ya mutu saboda Najeriya, yana mai cewa shugabanci na gaskiya na buƙatar sadaukarwa wajen magance matsalar tsaro.
Babban jami'in gwamna Soludo, Ben Nwankwo ya tsallake rijiya ta baya yayain da 'yan bindiga suka budewa tawagar shi wuta yana kan hanyar zuwa wani kauye.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya nuna goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Shugaban kungiyar Obidients Movement, Yunusa Tanko, ya yi martani kan batun cewa Peter Obi, ya rusa masallaci lokacin da yake kan kujerar gwamnan Anambra.
Anambra
Samu kari