Tsananin son jima’in wani mai gida ya sanya matarsa rugawa kotu don a raba aurensu

Tsananin son jima’in wani mai gida ya sanya matarsa rugawa kotu don a raba aurensu

- Ganin zata cuta saboda bukatar maigidanta ta nemi tallafin kotu

- Ta bayyana cewa matukar ba'a raba auren nasu ba, mijin nata na iya kashe ta

A ranar Larabar nan ne wata kotun dake da matsuguni a Iseyin ta raba wasu ma'aurata Baliki Oke da mai gidanta Arowolo masu kimanin shekaru 7 da aure bisa dalilin tsananin bukatar yin mu'amular aure da mijin yake da ita.

Tsananin son jima’in wani mai gida ya sanya matarsa rugawa kotu don a raba aurensu
Tsananin son jima’in wani mai gida ya sanya matarsa rugawa kotu don a raba aurensu

Hakan ya biyo bayan karar da Baliki ta shigar kotun, inda take rokon kotun da ta raba aurensu da mijinta Arowolo, sakamakon matsananciyar sha'awar da yake da ita wajen yin jima’i.

“Mai gidana yana kokarin hallaka ni, saboda tsanin karfin son yin jima'i, domin kuwa yafi girmama tare da son jima'i fiye abincin da zai ci a cikinsa, don a kullum yana iya saduwa da ni sau 6 a rana kafin ya samu gamsuwa".

KU KARANTA: Uba da 'Da sun yi taron dangin keta haddin wata Budurwa 'Yar shekara 13 a jihar Benuwe

“Kuma a duk lokacin da na yi kokarin hana shi, to sai ya yi min dan banzan duka, wannan ne ya sa na ke rokon wannan kotu da ta raba aurenmu domin tseratar da rayuwata".

Da kotun ta nemi karin bayani ga wanda akai karar wato Arowolo bai musanta zargin da matarsa tai masa ba, inda bayyana cewa “Na yi matukar kokarin ganin na raba kai na da wannan matsalar ta tsananin sha'awa, amma ya gagara".

Daga nan ne ya bukaci kotun da ta raba auren nasu, amma yayi alkawarin zai yi kokarin magance matsalar idan har matar tasa ta hakura ta dawo.

A karshe Alkalin kotun Adelodun Raheem ya yanke hukuncin raba auren, domin an gaza samun masalaha a tsakanin ma'auratan, tare da mikawa Baliki dan da suka haifa, bisa sharadin Arowolo zai dinga biyan Naira 2,500 a matsayin kudin ciyarwa duk wata.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng