‘Yan Sanda Sun Damke Yaro Mai Shekaru 17 da ya Dirkawa Mata 10 Ciki

‘Yan Sanda Sun Damke Yaro Mai Shekaru 17 da ya Dirkawa Mata 10 Ciki

  • Rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta bayyana yadda jami'anta suka yi nasarar cafke wasu da ake zargi da samarwa tare da siyar da jinjiraye
  • An ruwaito yadda aka kama wadanda ake zargin ranar Talata a wurare daban-daban tsakanin Obia zuwa Akpor da karamar hukumar Ikwerre
  • Jami'an sun ceto yara mata 10 dauke da juna biyu, sannan an gano yadda idan an haifi yaran ake ba kowaccensu N500,000 sannan a siyar da jinjirayen

Ribas - Rundunar 'yan sandan jihar Ribas a ranar Talata ta bayyana yadda jami’anta suka cafke wani yaro mai shekaru 17, Noble Uzuchi da Chigozie Ogbonna, mai shekaru 29 da suke aikin yi wa mata ciki a wani guri da aka haifa gami da siyar da jinjiraye.

Mai wa mata ciki
‘Yan Sanda Sun Damke Yaro Mai Shekaru 17 da ya Dirkawa Mata 10 Ciki. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Punch ta rahoto cewa, haka zalika, an kama wasu mata biyu da ake zargi, Favour Bright mai shekaru 30; da Peace Alikoi mai shekaru 40, wacce ake zargi da zama shugabar harkallar.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Yi Kicibus Da Muggan Makamai a Hannun Wata Mata Da Namiji a Jihar Arewa

An ruwaito yadda hudun da ake zargi suke cin karensu ba babbaka tsakanin Obia zuwa Akpor da karamar hukumar Ikwerre na jihar.

Har ila yau, 'yan sandan sun labarta yadda suka ceto yara mata 10 masu juna biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin 'yan sandan, Grace Iringe-Koko, a wata takarda data fita a Port-Harcourt ranar Talata, ta ce an yi nasarar kamasu ne bayan samun labari, wanda rundunar tayi amfani da shi.

Kamar yadda takardar ta bayyana:

”A ranar Asabar, 7 ga watan Janairu, misalin karfe 4:45 na yamma, yayin amfani da wani bayanin sirri da rundunar 'yan sandan jihar Ribas suka samu, jami'an binciken sirri na sashin C41 sun kai samame daban-daban gidaje biyu a Igwuruta da yankin Omagwa. Inda ake boye yaran da ake safara."

'Yan sandan sun ce masu harkallar suna hayar Uzuchi da Ogbonna don yin lalata da yara mata gami da dirka musu ciki.

Kara karanta wannan

'Yan Sandan Anambra Sun Kama Matashi Kan Fada, Ya Mutu a Hannunsu

"Wadanda jami'an suka ceto guda 10 ne, kusan dukkansu na dauke da juna biyu.."

Iringe-Koko, babban jami'in 'yan sandan yankin, ya ce bincike ya bayyana yadda idan aka haifi 'jinjiri ta harkallar, shugaban sabgar sai ya aje jinjirin gami da biyanta N500,000.

Mai magana da yawun 'yan sandan ta bayyana yadda aka haifi wasu jinjiraye kwanakin baya, sannan aka siyar dasu.

A cewarta:

"Duk wadanda lamarin ya auku dasu sun fallasa yadda aka yaudaresu da sai da yaran saboda matsanancinyar bukatar kudi da suke. An gano wata mota kirar Honda Pilot Jeed, launin fara a wurin shugabar harkallar.
"An mayar da lamarin sashin binciken laifuka na jihar, sannan ana kokarin bincikowa tare da kamo wadanda suke siyan jinjirayen."

Bidiyon damisa tana shawagi a wurin shakatawa ya firgita jama’a

A wani labari na daban, bidiyon wata damisa katuwa Da ta shiga wani wurin shakatawa ta firgita masu kallo.

Amma abun mamaki, an ga yadda wadanda ke zaune suka yi mirsisi basu nuna damuwa ko fargabar ganin dabbbar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel