Rundunar 'yan sanda sun ceto wasu 'yan mata daga gidan sayar da jarirai
- Rundunar 'yan sanda ta afkawa wani gida da ake zargin ana sayar da jarirai a jihar Anambra
- An gano cewa, a gidan ana sato 'yan mata a yi musu ciki domin su haifi jariran da za a sayar
- Ana ci gaba da neman mata mai gidan da aka yi basaja zuwa mashaya da gidan badala a yankin
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bankado wani gidan sayar da Jarirai a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin kasar, wanda ake yi masa badda kama a matsayin gidan shan barasa da mata masu zaman kansu a garin Nnewi dake jihar.
Rundunar 'yan sandan reshen jihar ta Anambra ta ce ta ceto wasu 'yan mata hudu masu juna biyu da ake jira su haihu yayin samamen da ta kai gidan, BBC Hausa ta ruwaito.
KU KARANTA: Dalilan da suka sanya jihar Kano haramta sayar da lemon dan tsami
Kakakin 'yan sandan jihar Haruna Mohammed ya ce kasuwancin da ake yi na sayar da barasa kawai wani basaja ne, inda daga ciki kuma ake kasuwancin sayar da jarirai a gidan.
Rundunar 'yan sanda ta ce Ikegwuonu wadda itace mai gidan ba ta da aiki sai kamo 'yan mata da gayyatar maza su yi musu ciki sannan a sayar da jariran da suka haifa nan take.
An kama wasu mata biyu da ke da alaka da gidan, kuma ana ci gaba da neman Gladys Nworie Ikegwuonu da ta gudu domin gurfanar da ita gaban shari'a.
KU KARANTA: 'Yan fashi sun far wa kwastoman banki da nufin kwace kudi N10m
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda ta Zamfara ta sake sauya jami’inta na 'yan sanda (DPO) da ke Kaura-Namoda, sakamakon zargin da ake yi masa da hada baki da ‘yan bindiga da ke addabar yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Mohammed Shehu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai, a Gusau a ranar Litinin.
Shehu ya ce, "an ja hankalin rundunar 'yan sanda ta jihar Zamfara zuwa wani bidiyo mai yaduwa a shafukan sada zumunta inda al'ummomin kauyen Kungurki, a karamar hukumar Kaura Namoda, suka zargi DPO na Kaura Namoda da hada baki da wasu 'yan bindiga.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng