Shugaban Sojojin Najeriya Ya Gana da Dakarun Sojin Kasar Rasha

Shugaban Sojojin Najeriya Ya Gana da Dakarun Sojin Kasar Rasha

  • Rahotanni na nuni da cewa Najeriya da Rasha sun bayyana shirin zurfafa haɗin gwiwa a harkar soja da fasaha
  • Bayan wata tattaunawa, kasar Rasha ta yaba da matsayin Najeriya a Afirka tare da ba da tabbacin goyon baya
  • Taron manyan hafsoshin ya mayar da hankali kan yaki da ta’addanci da musayar bayanan sirri domin tabbatar da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Rasha ta sake jaddada aniyarta ta zurfafa haɗin gwiwa da Najeriya a fannin tsaro da fasahar soji.

Wannan mataki yana daga cikin kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da daidaito a Nahiyar Afirka baki ɗaya.

Najeriya
Najeriya za ta zurfafa alaka da Rasha. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ganawar ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jakadan Rasha ya yi magana ne a wani taron manyan jami’an tsaro da ya gudana tsakaninsa da hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, da wasu jami’an sojin kasashen biyu.

Ya bayyana Najeriya a matsayin abokiyar huldar da ke da muhimmanci da makoma mai kyau a Afirka.

A cewarsa:

“Muna kallon Najeriya a matsayin ƙasa mafi girma a Afirka wacce ke da tasiri.
"Muna maraba da kokarinku na karfafa rundunar sojin ku domin kare kima da martabar ƙasarku da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankinku.”

Rasha ta yaba da jajircewar Najeriya

Wakilin ya nuna jin daɗinsa da yadda Najeriya ke da niyyar yin ingantacciyar haɗin gwiwa da Rasha a fannoni da suka shafi horar da sojoji da kuma fasahar yaki.

Ya bukaci a ci gaba da tattaunawa kai tsaye domin fayyace manyan abubuwan da ke gaban bangarorin biyu a fannin tsaro.

Jakadan ya kuma ba da tabbacin cewa Rasha za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya da sauran ƙasashen Afirka wajen yaki da kalubalen tsaro.

Janar Musa ya gode da taimakon Rasha

A nasa bangaren, Janar Musa ya nuna jin daɗinsa da irin tallafin da Rasha ke bai wa Najeriya, musamman wajen yaki da ta’addanci a cikin gida da yankin Afrika.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya gode wa gwamnatin Rasha bisa gayyatarsa zuwa bikin murnar cika shekaru 80 da Rasha ta yi nasara a yakin duniya.

Janar Musa ya ce:

"Muna daraja dangantakarmu da Rasha, kuma muna godiya da irin taimakon da kuke ba mu,”

Ya jaddada cewa Rasha ta kasance ƙasa mai cika alkawari kuma tana aiki domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Janar Musa
Janar Musa ya godewa Rasha kan tallafawa Najeriya. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Ana fatan taron zai haifar da sababbin yarjejeniyoyi da za su bunkasa fannonin horo, sufuri, samar da makamai da musayar bayanan sirri.

Shugaban sojin Najeriya ya koma Borno

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban sojin kasan Najeriya ya tare a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.

Hakan na zuwa ne yayin da barazanar kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram ke karuwa musamman a Borno da Yobe.

Ana sa ran matakin zai karfafa sojojin Najeriya da suke gwabza fada da 'yan ta'addan ISWAP da Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng