Gwamnatin Tarayya Ta Yi Bayani a kan Korar Wasu Ministoci

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Bayani a kan Korar Wasu Ministoci

  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ba a kori Ministan tsaro, Karamin Ministan tsaro da Ministan makamashi daga mukamansu ba
  • Mai ba wa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya bayyana cewa labarin da ke yawo ba shi da tushe ko makama
  • Onanuga ya roki jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa a kan shafukan da ke yada labaran karya ba tare da wani bincike ba
  • Hadimin shugaban kasan ya ce dole ne a hukunta masu yada labaran karya domin kare yancin fadin albarkacin baki na gaskiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Gwamnatin tarayya ta karyata rahotannin da ke cewa an kori wasu Ministoci uku daga mukamansu a gwamnatin Bola Tinubu.

Rahotannin sun ce an sallami Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle da Ministan makamashi, Adebayo Adelabu.

Matawalle
Gwamnati ta karyata korar wasu Ministoci Hoto: Dr. Bello Matawalle/Bayo Onanuga/Mohammed Badaru
Asali: Facebook

Sai dai a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abin takaici ne yadda wasu kafafen yada labarai ke watsa bayanai marasa tushe da sahihanci, suna fakewa da yancin fadin albarkacin baki.

Gwamnatin Tinubu ta karyata korar Ministoci

Bayo Onanuga ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba ta kori wadannan Ministocin ba inda ya shwarci masu yada labaran karya da su shiga taitayinsu.

Ya bukaci jami’an tsaro da su dauki mataki cikin gaggawa a kan wadannan shafukan da ke yada labaran karya.

Adebayo
Ministan makashi Adebayo Adelabu Hoto: Adebayo Adelabu
Asali: Facebook

Onanuga ya kara da cewa:

“Dole ne jami’an tsaro su gaggauta daukar mataki a kan shafukan yanar gizo da ke yada labaran karya da wadanda ke tallata su ba tare da tantance gaskiyarsu ba.

A hukunta masu yada labaran bogi - Gwamnati

A kari bayaninsa, hadimin shugaban kasa ya ce yana da matukar muhimmanci a dauki yada labaran karya a matsayin babban laifi da zai dace a hukunta masu aikata hakan.

Shafin X na Renewed Hope UK ya shawarci yan Najeriya da su guji daukar labarai daga shafukan da ba a aminta da su ba.

A bayaninsa, Onanuga ya ce idan ba a hukunta masu yada irin wadannan labarai ba, to za a ci gaba da barazana ga mutuncin kafafen yada labarai da kuma yancin fadin albarkacin baki na yan kasa.

A cewarsa:

“Yancin aikin jarida da fadin albarkacin baki ba zai yi tasiri ba idan wasu mutane na iya tashi su kirkiri labarai da labarun da ba su da tushe. Yada labaran karya rashin da’a ne, kuma dole ne a dauke shi a matsayin laifi.”

'Ana kashe kudi a kan wutar lantarki,' Gwamnati

A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin tarayya ta ce ta yanke shawarar gina tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa don rage kashe kudi.

Daraktan hukumar makamashi ta ƙasa (REA), Mustapha Abdullahi, ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da kashe Naira biliyan 47 a duk shekara wajen biyan kudin lantarki a fadar Villa ba.

A cewar Mustapha, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 10 domin gina wannan sabuwar tasha ta solar a Aso Villa don magance matsalar kudin wuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.