Ganduje Ya Ballowa Kansa Ruwa, An Yi Masa Rubdugu kan Kalamansa kan Tsarin Jam'iyya 1

Ganduje Ya Ballowa Kansa Ruwa, An Yi Masa Rubdugu kan Kalamansa kan Tsarin Jam'iyya 1

  • Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya jawo maganganu bayan ya bayyana goyon baya ga tsarin jam'iyya daya a Najeriya
  • A yayin wata hira da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, Ganduje ya ce samun jam'iyyu barkatai suna dagula harkar gudanar da gwamnati
  • Tuni jam'iyyar NNPP, kungiyar farar hula da manyan yan kabilar Ibo suka bayyana kalaman a matsayin barazana ga dimokuradiyya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya fuskanci suka bayan kalamansa da ke nuna cewa jam’iyyarsu ba ta da matsala da Najeriya ta koma ƙasar da ke da jam’iyya guda.

Ganduje ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma’a.

Ganduje
An soki kalaman Ganduje kan mayar da Najeriya tsarin jam'iyya 1 Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito Ganduje ya kara da cewa idan ‘yan Najeriya suka karkata zuwa jam’iyyar mai mulki, ba wanda zai ƙi ko ya yi takaddama da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ce tsarin jam’iyyu da dama na lalata shugabanci, yana mai cewa a yau, kasar Sin na daya daga cikin ƙasashe mafi ƙarfi a duniya, kuma tana amfani da tsarin jam’iyya guda.

NNPP ta caccaki kalaman Abdullahi Ganduje

Jam’iyyun adawa, kungiyoyin fararen hula da masu fafutukar dimokuraɗiyya sun yi Allah-wadai da kalaman Ganduje tare da zargin APC da barazana ga dimokuraɗiyya.

Adawa
Dungurawa ya ce bai yi mamakin kalaman Ganduje ba Hoto: Mustapha Kakisu Yalwa
Asali: Facebook

Ya ce:

“Ban yi mamakin tunanin Ganduje game da tsarin jam’iyya ɗaya ba, domin hakan yana nuna rashin mutunta akidun dimokuraɗiyya.”
“Idan wani mai riƙe da madafun iko ya raina sauran jam’iyyu ko ra’ayoyinsu, hakan na haifar da matsala ga tsarin mulki, Dimokuraɗiyya na buƙatar a bar kowa ya yi ra'ayinsa, haɗin kai da girmama sauran ‘yan siyasa.”

Dungurawa ya bukaci Ganduje da ya janye kalamansa, yana mai cewa hakan na iya haifar da rabuwar kai da rashin fahimta maras amfani.

Kungiyoyi sun yi tir da shugaban APC

Daraktan gudanarwa kungiyar CHRICED, Dr Ibrahim Zikirullahi, ya ce kalaman shugaban APC wata alamar barazana ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya.

Ya ce:

“Da a ce PDP, wacce ta mulki Najeriya daga 1999 zuwa 2015, ta tafi kan tsarin jam’iyya guda, da ba za a taba samun gwamnatin APC ba a yau. Wannan ra’ayi ba za a iya karɓarsa ba, kuma rashin kishin kasa ne ga wanda ke da wannan tunani.”

Ndigbo ta yi watsi da zancen Ganduje

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, Ezechi Chukwu, shi ma ya yi watsi da duk wani yunƙuri na komawa tsarin jam’iyya guda.

Ya bayyana cewa wannan mataki da wasu yan siyasa ke marari ya saba da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ganduje ya yiwa kujerar gwamna barazana

A baya, mun ruwaito cewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen mulkin jam’iyyar APGA a jihar Anambra ƙarƙashin Charles Soludo.

Ganduje ya fadi haka ne a yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar Anambra tare da 'yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa (NWC), a shirinsu na zaben fitar da gwani.

Ziyarar Ganduje ta zo daidai da ƙaddamar da sabuwar sakatariyar APC a jihar, wacce Sir Paul Chukwuma ya gina, kuma aka sanya wa kayan aiki ƙarƙashin Obiora Okonkwo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.