Abin da Ƴan Zamfara Suka Faɗawa Tinubu, Matawalle bayan Kisan Manyan Ƴan Bindiga
- Mutanen da ke zaune a karamar hukumar Talata Mafara sun godewa Bola Tinubu da Bello Matawalle kan kokarin da suke yi kan harkokin tsaro
- Mazauna yankin musamman suka kira sunan Tinubu da Matawalle saboda kashe shahararrun 'yan bindiga, Jijji Ɗan Auta da Kachallah Sagili
- Wani Yakubu Ibrahim Mafara ya ce mutuwar su ta kawo sauƙi da fata na samun zaman lafiya bayan shekaru na tashin hankali
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Talata Mafara, Zamfara - Wasu mazauna jihar Zamfara sun kuma tura godiya ta musamman ga Bola Tinubu da ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Al'ummar karamar hukumar Talata Mafara sun nuna gamsuwa ga Tinubu da Dr Bello Matawalle kan kokari a harkar tsaro.

Asali: Twitter
Ƴan Zamfara sun yabawa Tinubu, Matawalle
Leadership ta ce mutanen sun kuma yabawa mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk wannan godiya na zuwa ne bisa rawar da suka taka wajen kawar da hatsabiban 'yan bindiga biyu.
Harin da aka kai ya yi wa Jajji Ɗan Auta da Kachallah Sagili kaca-kaca, kuma jama’a sun yaba da wannan mataki a matsayin wata alama ta dawo da zaman lafiya.
Wanda ya yi magana da yawun al’ummar Talata Mafara, Yakubu Ibrahim Mafara shi ya bayyana haka a yau Juma'a.
Mafara ya ce sun yaba wa ƙoƙarin gwamnati da jami’an tsaro wurin ganin an murƙushe yan ta'adda.
Ya ce:
“Muna matuƙar godiya ga Matawalle, Tinubu, Ribadu da sauransu, muna farin ciki da fatan alheri bayan kai harin."

Asali: Facebook
Yadda aka hallaka ƴan bindiga a Zamfara
Sanarwar ta nuna tasirin wannan harin a kan al’ummar yankin da suka dade suna fama da ta’addancin 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Harin ya faru ne ranar Alhamis a Maikwanugga, wani yanki da ke cikin karamar hukumar, inda jami’an tsaro da masu aikin sa-kai suka gudanar da sintiri.
Sanarwar ta ce rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe Jijji Ɗan Auta da Kachallah Sagili, 'yan bindiga da ake tsoro sosai a yankin.
Sanarwar ta ce:
"Mutuwar su ta kawo sauyi a yankinmu, wanda ya shafe shekaru yana fama da tashin hankali."
Godiya da al’ummar suka nuna na nuni da yadda suke sake samun kwarin gwiwa ga shirin gwamnati na kawar da matsalar rashin tsaro, cewar Vanguard.
Sintirin da aka yi a yankin Talata Mafara wani bangare ne na shirin karya cibiyoyin 'yan bindiga da dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara.
"Kashe Jijji Ɗan Auta da Kachallah Sagili zai raunana ƙarfinsu matuƙa a wannan yankin namu."
- A cewarsa
Tattaunawar Legit Hausa da mazaunin yankin
Wani matashi Mubarak Musa da ke Talata Mafara ya yi tsokaci kan lamarin.
Musa ya ce bai kamata wata kungiya ko mutane su yi magana ya zama duk matsayar yan garin ba.
"Ba zai yiwu kungiya ko wasu mutane su yi magana da bakin duka al'umma ba, ya kamata su tsaya matsayin kungiya."
- Cewar Musa
Ya ce a halin da ake ciki a Zamfara babu mai yabawa Bola Tinubu ko Bello Matawalle da sauran jami'an tsaro.
Mazauna Zamfara sun yabawa Tinubu, Matawalle
Kun ji cewa mazauna Anka a jihar Zamfara sun yaba wa Bola Tinubu, Bello Matawalle da Janar Christopher Musa kan hallaka babban ‘dan bindiga, Mati.
Shugaban wasu al'ummar Anka, Muhammed Usman shi ya yi godiya ga Matawalle bisa taimakon sojoji wajen farmakin da ya hallaka ‘yan bindigar.
Sojoji sun gudanar da farmakin ne a karkashin "Operation Munzo", suka kwato makamai da lalata sansanonin 'yan bindiga a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng