Duniya Labari: Maniyyata Uwa da Ɗa daga Jihar Kano Sun Mutu a Hatsarin Mota

Duniya Labari: Maniyyata Uwa da Ɗa daga Jihar Kano Sun Mutu a Hatsarin Mota

  • Hukumar jin dadin Alhazai ta Kano ta sanar da mutuwar wasu maniyyata biyu da suka rasu sakamakon hatsarin mota
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a yankin Rimin Gado da ke jihar wanda ya jawo kimani a tsakanin mutane
  • Rahoton ya ce Alkasim Ibrahim-Walawa mai shekaru 48 da mahaifiyarsa Hadiza Garba mai shekaru 73 suna kan hanyarsu ta shirye-shiryen aikin hajji

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - An shiga jimami a jihar Kano bayan samun hatsarin mota wanda ya yi sanadin mutuwar wasu maniyyata.

Hukumar jin dadin Alhazai ta Kano ta sanar da mutuwar maniyyatan biyu da suka rasu sakamakon hatsarin mota.

Uwa da danta sun mutu a hatsarin mota a Kano
Taswirar jihar Kano da aka samu rasa rayukan maniyyata uwa da ɗanta a Kano. Hoto: Legit.
Source: Original

Kano: An rasa maniyyata uwa da ɗanta

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi, ya fitar a shafinta na Facebook a yau Talata 21 ga watan Afrilun shekarar 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

An budewa jirgin Faransa wuta da zai wuce ta Hormuz da Iran ta toshe

Sanarwar ta bayyana cewa hatsarin motar ya rutsa da ɗa da mahaifiyarsa wanda ya faru a yankin Rimin Gado da ke jihar Kano.

Mamatan su ne Alkasim Ibrahim-Walawa mai shekaru 48 da mahaifiyarsa Hadiza Garba mai shekaru 73 lamarin da ya rikita jama'a duba da girman rashi da iyalansu suka tafka.

An ce su biyun ‘yan asalin kauyen Walawa ne da ke karamar hukumar Kabo a Kano, kuma suna cikin shirin tafiya aikin hajji kafin hatsarin ya faru.

An tabbatar da cewa Alƙasim ya bar mata biyu da ’ya’ya bakwai, yayin da mahaifiyarsa ta bar ’ya’ya biyar a duniya.

Hukumar ta bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, inda ta ce sun rasu ne a lokacin da suke shirin tafiya ibada mai tsarki.

Maniyyata daga Kano sun yi mutu a hatsarin mota
Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle. Hoto: Kano Pilgrims Welfare Board.
Source: Facebook

Hukumar Alhazan Kano ta yi ta'aziyya ga iyalan

Hukumar ta yi addu’ar Allah ya gafarta musu, ya kuma sanya su cikin Aljannatul Firdaus, tare da jajanta wa iyalan da abin ya shafa, tana mai kira gare su da su yi haƙuri da juriya a wannan lokaci mai wahala.

Dederi ya ce rasuwarsu abin takaici ce matuka domin suna kan tafiya mai albarka da niyyar zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajji.

Kara karanta wannan

Bayan zuwan Amurka, kasar Musulunci za ta kafa cibiyar soji a Najeriya

Hukumar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da rokon Allah ya ba su juriya da hakuri wajen jure wannan babban rashi.

Mutane da dama kan tofa albarkacin bakinsu game da hatsarin inda suka bayyana jimami da alhini kan iftila'in tare da yi masu fatan samun rahama.

Mataimakin kakakin majalisa ya yi hatsari

A wani labarin, an ji cewa wani mummunan hatsarin mota ya rutsa da mataimakin kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Muhammad Adamu Oyanki.

Majiyoyi sun nuna cewa duk da motar da yake ciki ta yi kaca-kaca, Hon Oyanki ya tsira kuma yana cikin koshin lafiya.

Kakakin Majalisar Dokokin Nasarawa, Rt. Hon. Dr. Danladi Jatau, tare da wasu ‘yan majalisa, sun kai ziyara domin duba motar da aka yi hatsarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.