Hormuz: Ana Zargin Dakarun Iran Sun Buɗe wa Jirgin Ruwan da Ya Yi Kunnen Ƙashi Wuta
- Dakarun IRGC sun bude wuta a kan jirgin dakon kaya da ya yi biris rufe Mashigar ruwa ta Hormuz da Iran ta yi
- Harin bai janyo asarar rai ko gurbatar muhalli ba, amma ya kara dagula halin tsaron yankin bayan Amurka da Iran sun ja daga
- Lamarin ya zo ne bayan sabanin da ke tsakanin Iran da Amurka ya kara tsananta kuma ana ƙoƙarin shawo kan ƙasashen su yi sulhu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Iran – Dakarun rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran, wato IRGC, sun bude wuta a kan wani jirgin dakon kaya da ke bi ta mashigar Hormuz, lamarin da ya janyo lalacewa sashen jirgin.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru da misalin 7.55 na safiyar ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu na shekarar 2027 inda wani karamin jirgin yaki na rundunar ya kai harin kai tsaye ba tare da gargadi ba.

Source: Getty Images
New York Post ta wallafa cewa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya ce ta tabbatar da harin da aka kai wa jirgin ba tare da an ankarar da ita ba.
Kasar Iran ta buɗe wa jirgi wuta
The Times of India ta wallafa cewa bayan an yi kiran gargadi ga jirgin, sannan aka bude masa wuta tun saboda take gargaɗin da Iran ta bayar na farko kan rufe hanyar.
Sai dai duk da tsananin harin, ba a samu asarar rai ba, kuma babu wata illa da ta shafi muhalli da aka ruwaito ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Wannan na nuna cewa harin ya fi karkata ne wajen tsoratarwa da nuna karfin iko a yankin mai matukar muhimmanci ga kasuwancin duniya da Iran ta ja kunnen a kai.
Muhimmancin Hormuz ga duniya
Mashigar ruwa ga Hormuz na daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya, inda manyan jiragen dakon mai da kayayyaki ke bi kullum.
Duk wani rikici a wannan yanki na iya shafar farashin mai da tattalin arzikin duniya baki daya, inda kusan dukkanin ƙasashe za su ji a jikinsu.
Harin na baya-bayan nan ya zo ne a lokacin da ake fuskantar karin takun saka tsakanin Iran da Amurka, bayan Donald Trump ya yi kaka-gida a wani bangare na tekun.
A kwanakin baya, rahotanni sun bayyana cewa sojojin Amurka sun kwace wani jirgin dakon kaya na Iran bayan sun bude masa wuta, sannan suka shiga wani jirgin dakon mai da ake dangantawa da kasuwancin man Iran a tekun Indiya.

Source: Getty Images
Wannan jerin matakai na nuna yadda rikicin ke kara tsananta tsakanin kasashen biyu, musamman a bangaren tsaro da harkokin ruwa da ake bi wajen dakin mai.
Har ila yau, rahotanni sun nuna cewa an shirya tattaunawar tsagaita wuta a Pakistan, amma ba a kai ga nasara ba, lamarin da ya kara haifar da damuwa kan yiwuwar rikici mai girma a yankin.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, gwamnatin Iran ba ta fito bayyana cewa ita ce ta kai wannan hari ba ko akasin haka.

Kara karanta wannan
"Abu 1 muke tsoro," Qatar ta tsoma baki kan batun tattaunawar sulhun Amurka da Iran
Iran na shirin karo da Amurka
A baya, kun samu labarin cewa rundunar sojin Iran ta ce tana cikin cikakken shirin ko-ta-kwana, tana jiran duk wani hari daga dakarun ƙasar Amurka idan aka tabo su.
Kasar Iran ta bayyana cewa za ta mayar da martani ta hanyar kai hari nan take kan wuraren da aka riga aka tsara idan aka auka mata ba gaira ba dalili.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasar Amurka Donald Trump kan tsawaita tsagaita wuta da kuma ci gaba da sa takunkumi a kan jiragen ruwan Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

