Rikicin ADC: Nafi'u Bala Ya Fito da Dalilin da Ya Jawo Ƙauracewa Taron da Ya Shirya
- Nafi'u Bala mai ikirarin cewa shi halastaccen shugaban ADC na ƙasa ya musanta cewa kowa ya guji babban taron jam'iyyar
- A ranar Talata, 21 ga watan Afrilu na shekarar 2026 ne Nafi'u Bala ya kira babban taron jam'iyya na ƙasa a birnin tarayya Abuja
- Sai dai ba a ga kowa a wajen taron ba, lamarin da ya sa aka fara raɗe-raɗin ko jama'a sun ɗauke ƙafa ne saboda ba a tare da shi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsagin Nafi'u Bala na ADC, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa an kaurace wa babban taron ƙasa na jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, 2026.
Kakakin bangaren, Sani Bala, ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne cewa wakilai sun ƙi halartar taron da suka shirya a babban birnin tarayya Abuja.

Source: Twitter
A hira da ya yi da tashar AIT, ya ce a maimakon haka, an dage taron ne saboda jiran hukuncin da ake sa ran Kotun Ƙoli za ta yanke kan rikicin shugabanci da ke tsakanin bangarorin biyu na jam’iyyar.
ADC: An dage taron su Nafi'u Bala
Sani Bala ya bayyana cewa tun a baya, shugabansu, Nafiu Bala, ya riga ya sanar a wata hira da aka yi da shi cewa ba zai yiwu a gudanar da taron kamar yadda aka tsara ba.
A cewarsa, an dauki matakin ne domin kauce wa saba umarnin kotu da ke duba rikicin shugabancin jam’iyyar da ake fama da shi.
Ya kara da cewa matakin dage taron ya kasance bisa doka da kuma mutunta tsarin shari’a, yana mai cewa bangaren nasu ba zai aikata wani abu da zai saba wa umarnin kotu ba.
Za a sake shirya taron ADC

Kara karanta wannan
ADC ta gano barazana a dawo da ƴan ta'adda cikin jama'a, ta gargaɗi gwamnatin Tinubu
Kakakin Tsagin jam'iyyar ya kara da bayyana cewa za a sanar da sabuwar rana nan gaba da za a gudanar da taron.

Source: Facebook
Sani Bala ya kuma bai wa ƴan jam’iyyar tabbacin cewa za a sanar da sabuwar ranar gudanar da taron cikin lokaci domin ba su damar yin shiri yadda ya kamata.
Ya ce:
“Za a sanar da sabon rana nan gaba kadan bayan an kammala shari’ar da ke gaban Kotun Ƙoli."
Rikicin shugabanci a ADC ya dade yana haifar da rarrabuwar kai tsakanin ƴan jam'iyya inda kowane bangare ke ikirarin halaccin shugabanci.
Wannan rikici ne ya kai ga shari’ar da ke gaban Kotun Ƙoli, wacce ake sa ran za ta yanke hukunci kan wanda ya cancanci jagorantar jam’iyyar.
Nafi'u ya yi watsi da kiran Kwankwaso
A baya, mun wallafa cewa daya daga cikin jiga-jigan ADC, Nafi’u Bala ya bayyana cewa ba haka kawai ya yi fatali da kiran da Sanata Rabiu Musa Kwankwas ya yi masa ba.
Ya bayyana haka ne a dai-dai lokacin da jagoran Kwankwasiyya ya bayyana takaicin yadda Nafi'u Bala yaki amsa gayyatar da aka yi masa don jin menene korafinsa.
Sai dai Nafi'u Bala ya zargi Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran shugabannin jam'iyya ƙarƙashin Sanata David Mark da yin kaka-gida a jamiyyarsu na bisa ka'ida ba.
Asali: Legit.ng

