Boko Haram Ta Sauya Salo, Ta Koma Amfani da 'Jirage' wajen Kai Hare Hare Borno

Boko Haram Ta Sauya Salo, Ta Koma Amfani da 'Jirage' wajen Kai Hare Hare Borno

  • Hon. Ahmed Jaha ya ce Boko Haram na amfani da jirage mara matuki wajen kai hare-hare a Borno, wanda sojojin Najeriya ba su da shi
  • Ya bayyana cewa manoma 10 ne aka kashe a mazabarsa, kuma Boko Haram na ƙara ƙarfi a Borno fiye da baya, ya nemi a dauki mataki
  • Shi kuwa Hon. Yusuf Gagdi ya ce 'yan ta'adda sun ƙwace tankokin soji 40, lamarin da ya ce yana bukatar daukin Shugaba Bola Tinubu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ɗan majalisar wakilai, Ahmed Jaha ya ce yanzu 'yan Boko Haram ta koma amfani da jiragen sama masu sarrafa kansu wajen kai hare-hare ga mazauna jihar Borno.

Ɗan majalisar mai wakiltar Damboa/Gwoza/Chibok a Borno, karkashin jam'iyyar APC, ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin zaman majalisa.

Hon. Ahmed Jaha ya ce Boko Haram sun koma amfani da jirage mara matuki wajen kai hare-hare
Zauren majalisar wakilan tarayya, Abuja. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta ce Ahmed Jaha ya bayyana hakan ne yayin da yake bada gudunmawa ga kudirin da Ahmad Satomi ya gabatar kan gobarar da ta tashi a barikin sojoji na Giwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Boko Haram sun matsa wa Borno da hare-hare

Bayan ga gobarar da ta lalata makamai a barikin, kudurin Satomi ya kuma shafi "ƙaruwar" hare-hare kan sansanonin soji a jihohin Borno da Yobe.

Ahmed Jaha ya ce makaman da 'yan ta'addan ke amfani da su sun fi na sojojin Najeriya karfi da kuma zama na zamani.

A cewar dan majalisar:

"A wani ɓangare na mazaba ta, an kashe manoma 10 da ke neman itacen girki, har yanzu ba a gano wasu biyar ba, yayin da uku ke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali."

'Dan majalisar ya kuma shaida wa majalisar wakilan cewa 'yan ta'adda sun kuma kai hari kan wasu manoma 14 a cikin garinsu da ke Chibok, inji rahoton The Guardian.

Boko Haram na amfani da jirage mara matuki

Hon. Ahmed Jaha ya bayyana cewa ya rasa mutane da yawa a mazabarsa saboda Boko Haram na amfani da jirage marasa matuki da ke ɗauke da makamai.

Ya ce:

"Suna amfani da jiragen sama masu sarrafa kansu da ke ɗauke da makamai waɗanda sojojin Najeriya ba sa amfani da su. A takaice dai, sun fi sojojin Najeriya tafiya da zamani."

Jaha ya ce Boko Haram na "kara kaimi" wajen yin ƙarfi a garuruwan Borno fiye da yadda lamarin yake a baya.

Ya yi gargadin cewa:

"Boko Haram, ISWAP ko duk sunan da kuke kiran su, sun fara dawowa. Ya kamata mu dauki mataki don kada mu koma zamanin da Boko Haram ta mamaye kananan hukumomi 22 daga cikin 27 na Borno."
Dan majalisa, Yusuf Gagdi ya ce 'yan ta'adda sun kwace tankokin yakin soji guda 40
Hon. Yusuf Gagdi, dan majalisar wakilai daga jihar Filato. Hoto: @YusufAdamuGagdi
Asali: Facebook

'Yan ta'adda sun kwace tankoki 40 na soji

'Yan majalisar sun yi ta magana game da hare-haren 'yan ta'adda a ƙasar, inda Hon. Yusuf Gagdi daga Filato ya ce 'yan ta'addan sun ƙwace sama da tankokin yaƙi 40 na sojoji a lokacin hare-hare kan sansanonin soji.

Hon. Gagdi ya ce dole ne Shugaba Bola Tinubu ya ɗora alhakin sakaci ga kwamandoji da manyan hafsoshin soji da sauran shugabannin hukumomin tsaro.

Ya jaddada cewa:

"Ana kashe 'yan Najeriya kullum. Daga arewa zuwa Kudu zuwa Gabas. Dole ne gwamnati ta yi abin da ya dace. Kudurin da muke zartarwa kullum bai isa ba."

Gagdi ya ƙara da cewa sai majalisar ta yi magana a madadin 'yan Najeriya ta hanyar ɗora wa gwamnati alhaki, domin 'yan majalisar ba za su tsira daga fushin jama'a ba.

'Yan Boko Haram sun kashe sojoji a Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji a Buni Yadi, inda suka kashe sojoji huɗu tare da ƙona kayan yaƙi.

Harin ya faru ƙasa da awanni 24 bayan taron gwamnonin Arewa maso Gabas kan yaki da ta'addanci a Damaturu.

Wani soja da ya tsira ya ce maharan sun shiga sansanin da misalin ƙarfe 2:00 na safiyar Asabar, suka kwashe makamai, suka ƙona bindigogi, motoci, da MRAP biyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.