Yakin Iran: Isra'ila Ta Nuna Damuwa kan Kashe Babban Jami'in Leken Asirinta

Yakin Iran: Isra'ila Ta Nuna Damuwa kan Kashe Babban Jami'in Leken Asirinta

  • Rahotanni sun nuna cewa kasar Isra'ila ta fito ta bayyana wani babban jami'in leken asirinta da aka kashe yayin yakin da ta yi da Iran
  • Legit Hausa ta gano cewa shugaban Mossad, David Barnea ne ya bayyana haka yayin tunawa da jami'an leken asirin kasar da aka kashe
  • David Barnea ya kuma fadi gudunmuwar da marigayin ya bayar wajen karfafa ayyukan leken asiri da suka jawo wa Isra'ila nasara a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Isra'ila - Hukumar leken asiri ta Isra’ila, Mossad ta bayyana cewa wani babban jami’inta da ya taka muhimmiyar rawa wajen shimfida tubalin Operation Roaring King a kan Iran ya mutu a bakin aiki.

Yayin da yake jawabi a bikin ranar tunawa da jami’an leken asiri da suka rasu, Shugaban Mossad, David Barnea, ya bayyana jami’in da harafin farko na sunansa na Ibrananci, “Mem.”

Kara karanta wannan

An hango matsala: An hana ƴar siyasar Amurka da ke ƙin jinin Musulunci halartar taro

David Barnea a wajen wani taro
Shugaban hukumar leken asirin Isra'ila, David Barnea. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kashe babban dan leken asirin Isra'ila

Times of India ta rahoto cewa David Barnea ya yi magana yana mai cewa ya bayar da gudunmawa mai yawa ta hanyar jagorantar ayyuka masu sarkakiya.

“A wannan rana, ina tuna wa da jami’an Mossad da suka rasu da kuma zabin da suka yi na ba da gudunmawa tsawon shekaru wajen tsaron Isra’ila.”

In ji Barnea a wani bikin ranar tunawa a hedikwatar Mossad

Rahotanni sun nuna cewa irin wannan bayani abu ne da ba kasafai ake yi ba, domin Mossad ba ta cika bayyana asarar jami’anta ba.

Aikin da dan leken asirin ya yi

A cikin jawabin nasa, Barnea ya bayyana cewa yana alfahari da ayyukan da dan leken asirin ya yi, tare da cewa a kasar waje aka kashe shi.

“Zuciyata na tunawa da su tare da tattabar da cewa sun zama abin alfahari”
“Yayin Operation Roaring Lion, zuciyata da tunanina sun cika da alfahari da aikin ‘Mem,’ wanda ya mutu a wajen Isra’ila yayin da ya ke bakin aikinsa,”

Kara karanta wannan

Sojan Isra'ila ya yi wulakanci mai muni ga Yesu Almasihu, an fara sukar kasar

In ji Barnea, yana nuni da yakin baya-bayan nan da Iran.

Waye dan leken asirin da ya mutu?

Duk da haka, Isra'ila ba ta bayyana cikakken sunan jami’in ko takamaiman aikin da ya mutu a cikinsa ba saboda ka’idojin sirri na leken asiri.

A cewar rahoton Times of Israel, “Mem” yana cikin mutane hudu da suka nutse bayan wani jirgin ruwa ya kife a tafkin Maggiore da ke Italiya.

A lokacin, kafafen yada labarai na Italiya sun bayyana shi da suna Erez Shimoni mai shekaru 50, wanda ake zaton suna na bogi ne.

Benjamin Netanyahu a kasar Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yayin wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matsala ta tunkaro kasar Amurka

A wani labarin, kun ji cewa wani bayanin sirri da aka samu ya nuna cewa dakarun Amurka sun fara fuskantar karancin makamai masu linzami.

Hakan na zuwa ne bayan shafe kwana 40 suna gwabza yaki da Iran a Gabas ta Tsakiya, inda aka kai hare-haren a wurare da dama.

Wani rahoto ya nuna cewa Amurka ta fara shirin kara yawan makamanta, amma an ce zai iya daukar shekara hudu zuwa biyar kafin mayar da gurbi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng