Juyin Mulki: Za a Gurfanar da Ministan Buhari, Malamin Musulunci da Wasu a Kotu
- Rahoto ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta shirya gurfanar da wasu mutane da ake zargi suna da hannu a yunkurin juyin mulki a shekarar 2025
- Cikin wadanda za a gurfanar akwai tsohon ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva da malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Khalifa
- Gwamnatin tarayya ta zargi wasu daga cikinsu da rashin sanar da hukumomi shirye-shiryen juyin mulki da kuma karbar kudi ba bisa ka'ida ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhume guda 13 na cin amanar kasa kan mutane shida da ake zargi da hannu a wani shiri na hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanyar juyin mulki.
Hakan na zuwa ne bayan dogon lokaci da gwamnatin Najeriya ta dauka wajen bincike domi gano hakikanin abin da ya faru kan zargin.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji da tsohon minista suka raba miliyoyin Naira don kifar da gwamnatin Tinubu

Source: Facebook
Rahoton Vanguard ya nuna cewa a yau Laraba, 22 ga watan Afrilun 2026 za a gurfanar da su a gaban kotu idan ba an samu wani canji ba.
Juyin mulki: Wadanda gwamnati ke zargi da laifi
Wadanda aka shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja sun hada da tsohon karamin ministan albarkatun man fetur a zamanin marigayi Muhammadu Buhari, Timipre Sylva.
Manjo Janar mai ritaya Mohammed Ibrahim Gana; Kyaftin na rundunar sojin ruwa mai ritaya Erasmus Ochegobia Victor; dan sanda, Ahmed Ibrahim.
Sauran wadana ake zargi da za a gurfanar da su sun hada da Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da Sheikh Abdulkadir Sani Khalifa.
Daily Trust ta wallafa cewa, Sylva, wanda tsohon gwamnan jihar Bayelsa ne, yana cikin wadanda ake tuhuma kuma ya tsere a halin yanzu amma gwamnati na kokarin ganin an kamo shi.
Kudin da ake zargi sun karba
Dangane da wasu mu’amaloli, gwamnati ta ce Goni ya karbi jimillar Naira miliyan 50 da aka samu daga haramtaccen aiki, wato daukar nauyin ta’addanci, yayin da aka ce Sheikh Sani Khalifa ya karbi Naira miliyan 2.
Haka kuma, an ce Umoru ya karbi kudi Naira miliyan 10 ba tare da bi ta banki ba, sannan ya karbi karin Naira miliyan 8.8 da ake zargin kudin ta’addanci ne.

Source: Facebook
Rahoton ya nuna cewa akwai jami'i dan sanda, Ibrahim wanda shi ma ana zargin ya karbi Naira miliyan 1 da ke da alaka da wannan shirin.
A halin yanzu, idan babu wani sauyi da aka samu, ana sa ran za a gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik a yau.
An nemi a saki Sheikh Khalifa
A wani labarin, kun ji cewa wata kotu ta yi umarni da a saki malamin Musulunci, Sheikh Abdulkadir Sani Khalifa Zariya bayan watanni a tsare.
Hakan na zuwa ne bayan karar da aka shigar da wasu hukumomin Najeriya kotu kan tsare malamin na tsawon lokaci ba tare da gurfanar da shi ba.
Alkalin kotun ya bukaci hukumar EFCC, DSS, DIA da bankin Ja'iz su ba malamin diyyar miliyoyin Naira saboda tsare shi da rufe masa asusun banki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
