Yaki da Ta'addanci: An hango Sojojin Najeriya a Amurka, ana Masu Horo na Musamman

Yaki da Ta'addanci: An hango Sojojin Najeriya a Amurka, ana Masu Horo na Musamman

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa wasu jami'anta na karbar horo na musamman a Amurka a shirin yaki da ta'addanci
  • NAF ta bayyana cewa da zarar jami'an sun gama samun horo za su dawo gida bakin aiki domin cigaba da amfani da abubuwan da suka koya
  • Ta kuma bayyana irin horon da ake ba sojojin a jihar Ohio ta kasar Amurka domin su kawo sauyi a aikin soja idan suka dawo gida Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta fara horo na musamman kan kai dauki ta sama ga jami’an jinya nata a makarantar sojojin da ke Ohio a Amurka.

An gudanar da wannan horo ne ta hannun jami'an hadin gwiwar tsaro na ofishin jakadancin Amurka da ke birnin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

Matakin da Isra'ila ta dauka kan sojan da ya ruguza mutum mutumin Yesu

Wasu sojojin Najeriya a kasar Amurka
Sojojin Najeriya na samun horo a Amurka. Hoto: Nigerian Air Force HQ
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da horon da ake ba dakarun ne a wani sako da rundunar sojin saman Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.

Muhimmancin horon ga sojojin

Rahoto ya nuna cewa rundunar sojin saman ta bayyana cewa shirin horon zai kara karfafa ayyukan yaki da ta’addanci na NAF a fadin Najeriya.

Ta ce saurin kwashe wadanda suka ji rauni da kula da su a cikin jirgi na da matukar muhimmanci wajen ci gaba da aiki, kare rayukan jami’ai da kuma tabbatar da ingancin aikin soji a wuraren da ake fafatawa.

Horon da ake ba sojoji a Amurka

NAF ta ce horon zai ba da kwarewa ta musamman da ake bukata domin gudanar da aikin kwashe marasa lafiya ta sama yadda ya dace a tsarin karfin sojin sama na zamani.

Hakan ya hada da tsara aiki, bin ka’idojin tsaro da shirin ko-ta-kwana, sarrafa ma’aikatan jirgi, da kuma cikakken kula da marasa lafiya a cikin jirgi.

Kara karanta wannan

Za a kai wadanda suka shirya yi wa Tinubu juyin mulki kotu, an jero laifuffukansu

Yadda ake ba sojojin Najeriya horo a Amurka
Sojar Amurka na ba sojojin Najeriya horo. Hoto: Nigerian Air Force HQ
Source: Facebook

Ana gudanar da horon a cikin jirgi da ake gwaji da shi, inda ake koyar da matakan kafin tashin jirgi, yayin tafiya, da bayan sauka, tare da amfani da na’urorin likitanci da na binciken zamani.

An ce hakan yana kara karfafa hadin kai tsakanin aikin sojin sama da na kasa tare da tabbatar da sahihin tallafin jinya ga ayyukan yaki da sauransu.

Wasu jami'ai sun gama samun horo

NAF ta ce jami’ai biyu sun kammala wannan horo tare da dawowa, yayin da ake sa ran wasu za su tafi Amurka daga baya a cikin shekarar nan.

Bayan kammala horon, za a tura su zuwa sassan aiki domin amfani da kwarewarsu wajen inganta aikin kwashe marasa lafiya ta sama da kuma kare lafiyar jami’an soji gaba daya.

Trump ya tsayar da yakin Iran

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa ba za a cigaba da yaki da Iran ba bayan wa'adin tsagaita wuta ya kare.

Kara karanta wannan

Tsufa ya yi gardama: An kama tsoho dan shekara 60 na safarar bindigogi

Ya bayyana haka ne bayan gaza samun matsaya bayan tattaunawa da Amurka ta yi da Iran a Pakistan da gaza komawa sulhu karo na biyu.

Trump ya ce ya dauki matakin kara wa'adin yakin ne domin ba Iran damar sake nazari da kawo shawarar da za ta kawo karshen yakin gaba daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng