'Ƙarfi Ya Ci,' Iran Ta Yi abin Mamaki da Jiragen Dakon Mai 3 Suka Shiga Hormuz

'Ƙarfi Ya Ci,' Iran Ta Yi abin Mamaki da Jiragen Dakon Mai 3 Suka Shiga Hormuz

  • Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta sanar da kama jiragen ruwa guda biyu, MSC Francesca da Epaminodes da suka shiga Hormuz
  • Wannan mataki ya biyo bayan hare-hare har guda uku da aka kai wa jiragen ruwa daban-daban a cikin yini ɗaya, ciki har da jirgin Euphoria
  • Kakakin ma'aikatar wajen Iran, Esmail Baghaei, ya amince da tsawaita tsagaita wutar da Amurka ta yi, amma bai fadi ranar koma wa teburin sulhu ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran – Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya tabbatar da cewa dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙwace ragamar jiragen ruwa guda biyu waɗanda suka kai wa hari a safiyar yau Laraba a mashigar Hormuz.

Jiragen, waɗanda aka bayyana sunayensu a matsayin MSC Francesca da Epaminodes, yanzu haka ana jan su zuwa gaɓar tekun Iran.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Iran ta kama jirage 2 da suka shiga mashigr Hormuz
Jirgin yakin sojojin ruwan IRGC, Martyr Hassan Bagheri ya na tafiya a tekun Fasha. Hoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta kama jirage 2 a Hormuz

A cikin wata sanarwa, dakarun IRGC sun bayyana cewa jiragen sun "yi aiki ba tare da izini ba, sun keta ƙa'idojin zirga-zirga, kuma sun yi ƙoƙarin fita daga mashigar a ɓoye," wanda hakan a cewarsu ya kawo barazana ga tsaron teku, in ji rahoton CNN.

Ana kallon wannan mataki na Iran a matsayin martani ga Amurka wadda ita ma ta ƙwace jiragen Iran guda biyu a kwanakin baya.

Baya ga jiragen guda biyu da aka kama, kamfanonin yaɗa labaran Iran na Nour News da Fars sun bayar da rahoton hari na uku a kan wani jirgi mai suna Euphoria.

Birtaniya ta yi magana kan kama jirage

Rahoton ya bayyana cewa a yanzu haka jirgin ya "maƙale" a gaɓar tekun Iran, ko da yake ba su yi bayani dalla-dalla a kan yadda hakan ta faru ba.

Kara karanta wannan

Tofa: Iran ta kai sabon hari da zai iya rusa shirin tattaunawar sulhu da Amurka

Hukumar lura da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta tabbatar da cewa jiragen ruwan dakon mai sun fuskanci hare-hare waɗanda suka tilasta musu tsayawa a tsakiyar teku.

Sai dai, UKMTO ta ba ta sanar da ko an samu asarar rayuka, ko jikkatar mutane, ko lalacewar jiragen sosai ba, amma an ce wuta ta kama a jikin wasu.

Hukumar UKMTO ta Birtaniya ta ce Iran ta farmaki jiragen dakon mai uku a Hormuz.
Wani jirgin dakon mai a mashigar ruwan Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Martanin Iran kan tsagaita buɗe wuta

A ɓangaren diflomasiyya, kakakin ma'aikatar wajen Iran, Esmail Baghaei, ya yi magana game da tsawaita wa'adin tsagaita buɗe wuta da Shugaba Donald Trump ya sanar.

Baghaei ya bayyana cewa Iran za ta yi amfani da diflomasiyya ne kawai idan ta tabbatar da cewa za ta kare muradun ƙasarta da kuma dakile manufofin "maƙiya," cewar rahoton AP News.

Duk da amincewa da tsawaita wa'adin, Tehran ba ta fito fili ta bayyana cewa za ta halarci tattaunawar da ake shirin yi a Islamabad na ƙasar Pakistan ba.

Trump ya kara wa'adin tsagaita wuta

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran, yana mai cewa sojojin Amurka za su dakatar da harin da suka shirya.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗauki mataki kan buƙatar belin El Rufai, Malam zai zauna a hannun ICPC

A baya, Trump ya sanar da cewa bai san halin da za a shiga ba idan wa'adin mako biyu da aka yi ya kare, inda ya ce da wahala ya tsawaita yarjejeniyar.

Matakin kara wa'adin tsagaita wuta da aka dauka ya zo ne bisa bukatar masu shiga tsakani daga Pakistan, kamar yadda Trump ya yi ikirari a wani sako da White House ta sanar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com