Iran Ta Yanke wa Wani da Ke ba Isra’ila Bayanan Sirrinta Hukuncin Kisa

Iran Ta Yanke wa Wani da Ke ba Isra’ila Bayanan Sirrinta Hukuncin Kisa

  • Hukumomin Iran sun zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da ke yada bayanan sirrinta ga kasar Isra'ila da suke rikici
  • An kama mutumin mai suna Mehdi Farid da laifin yi wa Isra’ila leƙen asiri tare da tura bayanan sirri ga Mossad
  • Rahotanni sun ce marigayin ya yi aiki a wani bangare mai matuƙar muhimmanci na tsaron farar hula, inda ya yi amfani da damar da yake da ita

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wani mutum da aka samu da laifin leken asirin kasar.

An kama mutumin mai suna Mehdi Farid da yi wa Isra’ila leƙen asiri tare da tura mata bayanan sirri ga kungiyar Mossad.

Iran ta hukunta wani mai yada bayananta ga Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Rahoton Reuters ya tabbatar da cewa wasu kafofin yada labaran Iran sun bayyana cewa mutumin ya taba aiki a wani sashen tsaron farar hula.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Isra'ila ta nuna damuwa kan kashe babban jami'in leken asirinta

An kama 'yan Najeriya da laifin leken asiri

Hakan ya biyo bayan gurfanar da wasu yan Najeriya da ake zargin suna leken asirin Isra'ila da Amurka yayin da ake ci gaba da rigima a Gabas ta Tsakiya.

Wani shaida na hukumar DSS, ya fada wa kotu cewa wasu da ake zargi da ta’addanci sun amsa laifin leken asiri.

Mutumin ya tabbatar da cewa mutanen uku sun yi leƙen asiri kan ofisoshin jakadancin Amurka da Isra’ila a yakin da ake yi.

Ya ce wadanda ake tuhuma uku sun bayyana cewa sun je Iran domin samun horo kan makamai da tattara bayanan sirri kafin dawowa Najeriya.

An kashe wanda ke leken asirin Iran zuwa ga Isra'ila
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yayin taro a birnin Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Yadda aka gano mutumin da ke taimakawa Israila

Majiyoyi sun ce ya yi amfani da mukaminsa wajen tattara bayanai masu matuƙar muhimmanci sannan ya mika su ga hukumar leƙen asirin Isra’ila.

An ce kotun koli ta Iran ta tabbatar da hukuncin kisan bayan kammala dukkan shari’a kafin daga bisani a aiwatar da hukuncin kansa, cewar rahoton The Times of India.

Kara karanta wannan

Sojan Isra'ila ya yi wulakanci mai muni ga Yesu Almasihu, an fara sukar kasar

Hukumar ta ce an bi dukkan ka’idojin doka kafin zartar da hukuncin, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a duniya duba da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake fama da tashin hankali tsakanin Iran da Isra’ila kan batutuwan tsaro da siyasa.

Masana na ganin irin wadannan matakai na iya kara dagula alaka tsakanin kasashen biyu da kuma kara tsananta rikicin yankin.

Ukraine na zargin Rasha da taimakon Iran

A baya, an ji cewa Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy ya yi magana kan yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Zelenskiy ya ce kasarsa ta samu hujja karara cewa Rasha na bai wa Iran bayanan sirri, lamarin da zai kara tsawaita rikicin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban ya ce Rasha na amfani da fasahar tattara bayanan sigina da hadin gwiwa da wasu kasashen yankin domin taimaka wa Iran wajen kai hare-hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.