Kansililon Ganduje za Su Warwasa, Abba zai Biya Su N15.6bn da Suke Bin Gwamnati
- Gwamnatin Kano ta amince da biyan kansilolin da suka yi mulki a zamanin Abdullahi Umar Ganduje hakkokinsu
- Gwamna Abba ya amince da biyan Naira biliyan 15.6 ga kansiloli fiye da 3,000 daga kananan hukumomi 44 na jihar
- An tsara biyan kudin a watannin Afrilu, Mayu da Yuni 2025 domin farantawa jagororin da kananan hukumomin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da fitar da kudin da ya kai N15.6bn domin biyan kudaden fansho da sauran hakkokin tsofaffin kansiloli 3,000 daga kananan hukumomi 44 na jihar.
Hakkokin sun hada da kudin hutu da sauran alawus-alawus da ya cancanta a ba kansilolin da suka yi aiki a karkashin gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe a sanarwar da Ibrahim Adam, mai ba gwamna shawara kan harkokin yada labarai, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa wadannan tsofaffin kansiloli ba su samu hakkokinsu ba tun bayan karewar mulkinsu a karkashin gwamnatin Ganduje.
Dalilin gwamna Abba na biyan kansilolin Ganduje
A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano, wacce Legit ta gani, an ce za a biya kansilolin da suka yi wa’adin mulki a 2014-2017, 2018-2020, da kuma 2021-2024.
Sanarwar ta ce za a raba kudaden cikin kashi uku, kuma za a fara biyan su a cikin Afrilu, Mayu, da Yuni 2025, domin saukaka nauyin da ke kan gwamnati.

Asali: Facebook
Gwamnatin Abba ta bayyana cewa rashin biyan wadannan hakkoki na da matukar tasiri ga rayuwar tsofaffin kansilolin, wanda ya haifar da rashin jin dadi a zukatansu.
Gwamnan wanda ya hau mulki a karkashin jam’iyyar adawa ya dauki wannan matakin a matsayin cika alkawarin da ya dauka na dawo da mutuncin ma’aikatan gwamnati.
A cewar sanarwar:
“Amincewa da Naira biliyan 15.6 na daga cikin matakan Gwamna Abba Kabir Yusuf na cika alkawarin da ya dauka na tabbatar da cewa duk wani hakkin ma’aikatan gwamnati, musamman wadanda aka zaba, an biya su yadda ya dace. Hakan na daga cikin kokarin dawo da martabar masu aikin gwamnati.”
Gwamnatin Abba ta farantawa kansilolin Abba
Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Kano ta dauki gabarar biyan kudin domin a mutunta sadaukar da kai da shugabannin kananan hukumomi suka yi.
Sanarwar ta ce:
“Lokaci ya yi da za a gyara kura-kuran da suka gabata, kuma wannan gwamnati na da niyyar tabbatar da hakan.”
An ruwaito cewa jagororin kananan hukumomi da dama sun ji dadin wannan mataki na Gwamna Abba, suna kallonsa a matsayin wata dama ta gyara rashin adalcin da aka yi musu a baya.
Gwamnatin Abba ta biya 'yan fansho
A baya, mun wallafa cewa hukumar kula da kudin fansho ta Kano ta ce ta riga ta biya bashin da ya kai Naira biliyan 21 daga cikin jimillar Naira biliyan 28.6 da tsofaffin ma’aikatan jihar.
A cewar Fagge, akwai tsofaffin ma’aikata da aka dinga cire musu kudi ba bisa ka’ida ba a lokacin gwamnatin da ta gabata, har ma wasu lokuta ana cire rabin albashinsu ba tare da hujja ba.
Ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da biyan sauran basussukan da suka rage, domin rage radadin rayuwa da tsofaffin ma’aikata ke fama da shi saboda gaza biyansu hakkokinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng