An Fitar da Hotunan Yaran da ake ba Horo kan Jirage Marasa Matuka

An Fitar da Hotunan Yaran da ake ba Horo kan Jirage Marasa Matuka

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta fara horar da ɗaliban AFMS kan sarrafa jiragen sama marasa matuƙa da sauran fasahohin zamani
  • NAF ta ce horon zai taimaka wajen samar da sababbin ƙwararrun matasa domin tinkarar ƙalubalen tsaro da ci gaban fasaha a Najeriya
  • 'Yan Najeriya sun yaba da shirin, yayin da wasu suka buƙaci a bai wa yaran talakawa damar shiga irin wannan makaranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jos, Plateau – Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta bayyana cewa ɗaliban makarantar sojin sama (AFMS) da ke Jos na samun horo na musamman.

An nuna yadda daliban ke sarrafa jiragen sama marasa matuƙa kai tsaye da sauran sababbin fasahohin zamani da ake samar wa a duniyar yau.

Yadda ake sarrafa jirage marasa matuka
'Yan makarantar sojin Najeriya suna aiki da jirage marasa matuka. Hoto: NAF
Source: Facebook

Rundunar ta wallafa a Facebook cewa shirin na da nufin samar da sabbin ƙwararrun matasa masu ilimi, ƙwarewa da tunani na kirkire-kirkire domin su zama jagororin gobe a fannin tsaro da ci gaban ƙasa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga Kaduna da dare, sun kashe rayuka 30 sun kona gidaje

NAF ta fara gina ƙwararrun matasa

A cikin wani saƙo da ta wallafa, rundunar sojin sama ta ce ta hanyar koyarwa a aikace, horo mai inganci da tarbiyya, ana taimaka wa waɗannan matasa wajen samun ƙwarewa da ƙarfin guiwa da kuma dabarun magance matsaloli.

Rundunar ta ƙara da cewa hakan ya zo ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro, inda amfani da fasahar zamani ya zama muhimmin ginshiƙi wajen kare rayuka da dukiyoyi.

NAF ta ce habaka matasa tun suna kanana zai haifar da sababbin masu sarrafa jirage marasa matuka da shugabanni masu kishin ƙasa da sadaukarwa ga hidimar al'umma.

'Yan Najeriya sun yi martani

Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu bayan wallafa hotunan, inda wasu suka yaba da matakin, yayin da wasu suka yi kira da a faɗaɗa damar shiga makarantar.

Abdulaziz Lawal ya ce:
"Ina fata yaran talakawa ma za su samu damar yin karatu a nan, amma irin waɗannan damammaki kamar na masu kuɗi da 'yan siyasa ne kawai. Najeriya ba za ta taɓa zama ƙasa ɗaya ta wannan hanya ba.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani

"Saboda haka ina fatan ganin yara ne sun zama kamar waɗannan yaran."

Ex Bœ Holy Fundz ya ce:

"A kullum a shirye nake wajen bayar da gudunmuwa, ko da hakan zai jawo rasa raina."

Mohammed Toyin Salman ya ce:

"Ya kamata gwamnati ta ba su duk tallafin da suke buƙata."

Mark Gabriel ya ce:

"Idan aka fara gina su tun suna ƙanana, matsayin da za su iya kaiwa ba ta da iyaka."
Yan makarantar soji a Najeriya
Yadda ake ba 'yan makarantar sojin Najeriya horo. Hoto: NAF
Source: Facebook

Esson Isuwa ya ce:

"Idan muka haɗa kai, za mu iya sake gina ƙasarmu ta zama babba. Ban taɓa nadamar kasancewa ɗan Najeriya ba, kuma ina fata har a rayuwar gaba zan sake kasancewa ɗan Najeriya."

Abdulrazaq Dabo Dabai ya ce:

"Lallai wannan abin burgewa ne. Gaskiya abin farin ciki ne ganin matasanmu suna tasowa da irin waɗannan ƙwarewa."

NAF ta saye jiragen yaƙi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kammala gwajin karɓar rukunin farko na jiragen yaƙi kirar M-346 guda uku a ƙasar Italiya.

Kara karanta wannan

Najeriya ta saye sababbin jiragen yaki, za a zafafa yakar 'yan ta'adda

Rundunar ta bayyana cewa jiragen sun cika dukkan ƙa'idojin fasaha da tsaro, kuma ana sa ran za a kawo su Najeriya kafin watan Disambar 2026.

A bayanin da rundunar NAF ta yi, ta bayyana cewa an saye jiragen ne domin ƙarfafa ayyukan tsaron sararin samaniyar ƙasar nan baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng