Tagomashin Gwamnatin Kano Ya Kai ga Dalibai, An Raba Fam 10,000 na JAMB Kyauta
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon fam ɗin JAMB kyauta ga daliban sakandare 10,000 don ƙara bunƙasa ilimi
- Haka kuma gwamnan ya kaddamar da cibiyoyin da za a yi amfani da su don horas da dalibai kan yadda za su yi amfani da kwamfuta
- A jawabinsa yayin taron, Abba Kabir Yusuf ya ce za a zaɓa wa daliban da suka yi nasara manyan makarantu don su ci gaba da karatu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon fam ɗin JAMB guda 10,000 kyauta ga ɗaliban makarantun sakandare na jihar.
Haka kuma ya kaddamar da horaswa ga masu cin gajiyar shirin a kan amfani da kwamfuta a cibiyoyi daban-daban da aka keɓe a fadin Kano gabanin jarrabawar.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa a lokacin kaddamar da rabon, gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu wakilcin kwamishinan ilimi na jihar, Ali Haruna Makoda.
Kano: Abin da aka shiryawa masu rubuta JAMB
A jawabinsa, mashawarci na musamman kan harkokin ilimi ga gwamnan Kano, Tajuddin Gambo, ya ce gwamnati za ta samar da sufuri ga masu cin gajiyar shirin.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta zaɓi manyan makarantu ga waɗanda suka yi nasara a jarrabawa, tare da shawartarsu da su jajirce wajen karatu domin samun nasara.
Rabon fam ɗin JAMB ya biyo bayan rage 50% na kudin rajista a jami’o’i da cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare na jihar da bayar da gudunmawar kuɗi don inganta ilimin yara mata.
Gwamnatin Kano ta bayyana ayyukanta a bangaren ilimi
A wajen taron, Gwamna ya yi amfani da damar don yin bayanin nasarorin da gwamnati ta cimma wajen bunƙasa bangaren ilimi cikin watanni 22 da suka gabata.
Ya ce ayyukan sun haɗa da dawo da tallafin karatu zuwa ƙasashen waje da na cikin gida, sake buɗe cibiyoyin koyon sana’o’i guda 21 da gyara makarantun firamare da sakandare.

Asali: Twitter
Sauran ayyukan sun haɗa da ginin sababbin dakunan karatu, samar da kayan ɗakin karatu da kayan rubutu, da rabon kayan sawa kyauta ga ɗaliban makarantun firamare.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga ɗaliban da suka amfana da shirin su yi amfani da wannan dama ta hanyar da ta dace domin inganta rayuwarsu.
Hadimin gwamnan Kano ya rasu
A baya, mun wallafa cewa ana shiga alhini a Kano bayan samun labarin rasuwar wani matashi kuma mai taimaka wa gwamna Abba Kabir Yusuf a bangaren ci gaban matasa, Abdullahi Salisu Furfura.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya ta fitar a shafinta na Facebook, inda ta bayyana jimami da alhini bisa wannan rashi.
A cewar sanarwar, marigayin Abdullahi Furfura ya rasu ne kasa da sa’a guda bayan ya wallafa rubutu a shafinsa na Facebook, abin da ya kara daga hankalin jama'a a kan rashin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng