Kano: Bayan Kotu Ta Tsige Shi, Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Koma Sana'ar Dinki
- Tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano ya zaburar da matasa bayan an hango shi ya koma shago da ya rasa kujerarsa
- Kafin ya samu kujerar shugabancin da ya rasa a kotu, Abdullahi Gali Shitu fitaccen tela ne da ya kware a harkar dinka kaya a jihar Kano
- Ya bayyana cewa dama tun can da sana'arsa, ya kuma fadi yadda sana'ar dinkin ta biya masa kudin shiga harkokin siyasa da kamfen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, Abdullahi Gali Shitu, wanda aka fi sani da Comrade Abdullahi Gali Basaf, ya koma ci gaba da sana'arsa ta dinki bayan kotu ta kwace masa kujerarsa.
Basaf ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya nuna wa jama'a cewa bai kamata siyasa ta zama hanyar rayuwa kadai ba, domin kowa ya kamata ya mallaki sana'ar da za ta rike shi.

Source: Facebook
A hira da ya yi da jaridar DailyTrust, Basaf ya kara da cewa sana'ar dinki ta yi masa riga da wando, har da biyan harkokinsa na siyasa.
Basaf ya zaburar da matasan Kano
Trust Radio ta kawo labarim cewa Basaf ya kara da cewa bai dace masu harkokin siyasa su mayar da hankali a kanta kawai ba, ganin cewa ba ta dace ta zama hanyar azurta kai ba.
Ya ce:
"Na koma sana'ar dinki ne domin in isar da sako ga mutane cewa kada su mayar da hankali kan siyasa kadai."
Tsohon shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa ya fara sana'ar dinki tun yana matashi, kuma ya shafe sama da shekara goma yana gudanar da ita.

Source: Facebook
A cewarsa, yana sayen yadudduka, yana dinkawa sannan ya sayar da su da kansa. Duk da ya taba hada noma, fenti da kananan kasuwanci, ya ce dinki ce ta fi zama ginshikin rayuwarsa.
Ya ce:
"Dinki ba karamar sana'a ba ce. Babbar sana'a ce da ke ciyar da mutane. Har lokacin da nake siyasa, sana'ar dinki ce ta taimaka min wajen daukar nauyin yakin neman zabe da ayyukan siyasa. Da ba ita ba, da abin ya yi wuya."
Kiran Basaf ga matasan Kano
A halin yanzu, ya ce shagon nasa na daukar ma'aikata da almajirai kusan 20, yayin da burinsa shi ne ya fadada sana'ar zuwa kamfanin samar da tufafi da zai samar wa sama da mutum 50 aikin yi.
Basaf ya ce dawowarsa sana'ar dinki ba saboda rashin mafita ba ne, illa domin ya karfafa gwiwar matasa su mutunta sana'o'insu.
Ya ce:
"Sakona ga matasa shi ne kada su raina sana'o'i. Su daraja su kuma inganta su."
Ko da yake yana da digirin farko da na biyu a fannin Kimiyyar Siyasa, ya ce ya zabi komawa dinki ne saboda ita ce sana'ar da yake so kuma yake son bunkasa ta domin amfanin al'umma.
Basaf ya dauki nauyin dalibai
A wani labarin, mun wallafa cewa shugaban karamar hukumar Kumbotso, jihar Kano, Kwamared Abdullahi Ghali Basaf ya dauki nauyin dalibai 1,100 domin yin karatun da zai ba su kwalin NCE.
A yayin da ciyamomin Kano 44 suka cika kwanaki 100 a kan mulki a wancan lokaci, Kwamared Abdullahi Basaf ya lissafa ayyukan da ya shimfida a Kumbotso a yunkurinsa na samar da jagoranci.
Wannan yunkurin na shugaban karamar hukumar na zuwa ne yayin da gwamnatin Abba Kabir ta sake tura 'ya'yan talakawa karatu waje da kuma nanata cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban matasa.
Asali: Legit.ng


