'Aljihunsu Kawai Suka Sani': Baffa Bichi Ya Fara Sakin Maganganu kan Kwankwaso
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ya zargi gwamnatin jihar Kano karkashin jam’iyyar NNPP da fifita aljihunta a kan talakawa
- Baffa Bichi ya bayyana cewa shi da wasu ‘yan jam’iyyar NNPP sun fuskanci matsin lamba da tsangwama da suka bayyana a matsayin shakar mutuwa
- Duk da kasancewarsa a cikin NNPP da aiki tare da Rabi’u Musa Kwankwaso a baya, Baffa Bichi ya ce akidarsa da salon siyasar Madugun dabam da juna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ya zargi gwamnatin NNPP ta Kano da fifita makomar kansu a maimakon mayar da hankali wajen inganta talakawa.
Ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da wasu daga cikin masu goyon bayansa, kwanaki kaɗan bayan ya tabbatar da sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Asali: Facebook
A hirar da Premier Radio ta wallafa a shafinta na Facebook, Baffa Bichi ya bayyana cewa “shakar mutuwa aka yi mana a NNPP,” har aka tilasta musu barin jam’iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Kaddara ce ta haɗa ni da Kwankwaso,’ Bichi
Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana cewa zubinsa da akidarsa ba su da kamanceceniya da na jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Asali: Twitter
Tsohon Sakataren Gwamnatin ya ce:
“Karfi da yaji, shakar mutuwa aka yi mana har muka tafi. Saboda ai ni, tarbiyya ta, zubi na, da akida ta – kwata-kwata ba daya take da ta Kwankwaso ba.”
“Amma saboda shakar mutuwa da aka yi mana a gidanmu, muka rasa yadda za mu yi. Kaddara ce kawai ta sa muka je muka haɗu da Kwankwaso. Amma layin ba daya ba ne kwata-kwata.”
Bichi ya caccaki Gwamnatin Kano, Kwankwaso
Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ya zargi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamnatin Kano da saka aljihu a gaba, maimakon jama’a.
“Mu, jama’a muka sa a gaba; su kuma, aljihunsu suka saka a gaba. Akwai maganganun da idan muka fadi su, duk inda suka fita a titi, sai an yi masu intifada.”
Ya ce akwai hujjoji a hannunsu da ke tabbatar da cewa akwai badakala a gwamnatin Abba, wanda ya ninka wanda aka zargi gwamnatin Ganduje da aikatawa.
Ya shawarci magoya bayansa da su bayar da hadin kai, domin a hannu hannu domin samun nasara a sabuwar tafiyar da suka sanya a gaba.
Duk da zancen da ya yi a gidansa, 'dan siyasar ya nunawa magoya bayansa bai fara magana ba tukuna, ya ce idan ya soma, sai an fatattaki masu mulkin.
Yarbawa na neman hadin kan Kwankwaso
A baya, mun wallafa cewa kungiyar matasan Yarabawa ta ta bukaci Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da ya yi watsi da kiran da ake yi masa na shiga hadakar ‘yan adawa.
Shugaban kungiyar, Hammer Olalekan, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Ibadan, inda ya ce Sanata Kwankwaso babban dan siyasa ne da bai kamata ya zauna a matsayin dan adawa ba.
A cewar Olalekan, hadakar da wasu ke kokarin kafa wa a karkashin jagorancin Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai ba ta da karfi da tasirin da za su iya kayar da jam’iyyar APC da Tinubu a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng