Bayan Shafe Wata 2 a Hannunsu, Ƴan Bindiga Sun Hallaka Limami da Danginsa a Zamfara

Bayan Shafe Wata 2 a Hannunsu, Ƴan Bindiga Sun Hallaka Limami da Danginsa a Zamfara

  • 'Yan bindiga sun kashe wani babban limami, Malam Salisu da wasu 'yan uwansa biyu da suka yi garkuwa da su watanni biyu da suka wuce
  • Malam Salisu da danginsa sun kasance a hannun 'yan bindigar ne tun wata biyu da suka gabata kafin a kashe su
  • Wannan labari mai tayar da hankali da kara jefa al'umma cikin fargaba da bakin ciki a yankunan da ake fama da rikici
  • A halin yanzu, hare-haren 'yan bindiga na ci gaba da addabar al’ummomi da dama a jihar Zamfara ba tare da kakkautawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara- 'Yan bindiga da suka sace babban limami a jihar Zamfara sun yi ajalinsa wanda ya ta da hankulan mutane a yankin.

An sace marigayin Malam Salisu watanni biyu da suka wuce kafin kashe shi tare da wasu biyu daga cikin 'yan uwansa.

Yan bindiga sun yi ajalin limami a Zamfara
Bayan sace shi watanni 2 da suka wuce, yan bindiga sun hallaka limami a Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Bakatsine da ke nazari kan harkokin tsaro ya wallafa a shafin X a yau Talata 29 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An taso Dauda a gaba kan rashin tsaro

Wannan hare-haren na zuwa ne yayin da al'ummar jihar Zamfara ke kokawa kan yawaitar harin miyagu a yankuna daban-daban.

Hakan ne ma ya sa wata kungiya a yankin Neja-Delta, NDYC ta bukaci gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta baci a Zamfara saboda yawaitar kashe-kashe.

Kungiyar ta ce lamarin ya kai matakin da ake rasa tsaro kwata-kwata, mazauna yankin ke rayuwa cikin tsoro da fargabar rasa rayuka.

Sannan kungiyar NDYC ta jaddada cewa tun da aka ayyana dokar ta baci a Jihar Rivers, ya kamata a yi gaggawa a sa irinsa a Zamfara.

Yaushe aka sace limamin a Zamfara?

A daren ranar 12 ga watan Faburairun 2025, 'yan bindiga sun kai hari garin Maru, suka sace mutane da dama.

Daga cikin wadanda aka ɗauke akwai limamin garin, Malam Salisu da iyalansa wanda ya ɗaga hankulan jama'ar yankin.

Limami ya rasa ransa a hannun ƴan bindiga a Zamfara
Yan bindiga sun hallaka limami bayan shafe watanni 2 a hannunsu. Hoto: @DanKatsina50.
Asali: Twitter

Al'umma na cikin fargaba bayan kisan limamin

Wannan mummunan labari ya girgiza jama’a yayin da 'yan bindiga ke ci gaba da haddasa barna a sassa daban-daban na jihar Zamfara.

Mutanen da suka rasa rayukansu sun dade a hannun masu garkuwa da mutane kafin a kashe su ba tare da an ceto su ba.

A halin yanzu, al’umma da dama a Zamfara na rayuwa cikin tsoro yayin da hare-haren 'yan bindiga ke kara kamari a yankin.

Rikicin 'yan bindiga a Arewa

A 'yan shekarun nan, yankin arewacin Najeriya na fama da matsalar tsaro sakamakon yawaitar ayyukan 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Wannan matsala ta fi kamari a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto da Kebbi, inda rayuka da dukiyoyi ke salwanta kullum.

'Yan bindigar na kai hare-hare kan kauyuka, su na sace mutane, su na bukatar kudin fansa, sannan idan ba a biya ba, sukan kashe su ba tare da jin tausayin kowa ba.

Wannan matsala ta shafi rayuwar al’umma ta fuskar noma, kasuwanci da walwala, inda mutane da dama ke gudun hijira daga gidajensu saboda tsoro da rashin tsaro.

A cikin irin wannan yanayi ne aka sace babban limami Malam Salisu tare da wasu daga cikin 'yan uwansa a garin Maru na jihar Zamfara.

Bayan watanni biyu a hannun 'yan bindigar, an kashe su cikin zalunci, lamarin da ya kara jefa jama’a cikin fargaba da bakin ciki.

Hakan yana nuna yadda rashin tsaro ke kara ta'azzara a yankin, inda jama’a ke ganin babu wani kariya daga gwamnati.

Kungiyoyi da dama sun bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa, ciki har da ayyana dokar ta baci domin kare rayukan al’umma.

'Yan bindiga sun hallaka jami'in tsaro

A baya, mun ba ku labarin cewa wasu y bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a wasu ƙananan hukumomi guda uku na jihar Zamfara a cikin 'yan kwanakin nan.

Miyagun ƴan bindigan sun kashe mutane tare da yin awon gaba da wasu Bayin Allah masu yawa zuwa wurin da ba a sani ba.

Ƴan bindigan sun kuma kashe wani 'dan rundunar Askawaran Zamfara, aka sace abokin aikinsa bayan sun tare motarsu a hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.