Sola a Aso Villa: Gwamnati Ta Fadi Biliyoyin da Take Kashewa a Biyan Kudin Wuta

Sola a Aso Villa: Gwamnati Ta Fadi Biliyoyin da Take Kashewa a Biyan Kudin Wuta

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana shirin girka tashar sola a Aso Villa don rage yawan kuɗin wutar lantarki da take biya
  • Shugaban hukumar makamashi ta kasa ya ce gwamnati na kashe Naira biliyan 47 duk shekara a kudin wutar fadar Aso Rock
  • Domin rage kashe kudin gwamnati, an ce Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 10 don gina karamar tashar sola a cikin fadar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya sa za ta girke tashar wutar sola a Aso Villa, babban ofishin mulki na Najeriya.

Daraktan hukumar makamashi ta ƙasa, Mustapha Abdullahi, ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan Naira biliyan 47 a kowace shekara kan wutar lantarki a Villa ba.

Gwamnatin tarayya ta fadi kudin da take kashewa kan wuta a Aso Villa wanda ya sa za ta koma sola
Fadar shugaban kasa ta yi magana kan saka sola da biyan kudin wuta. Hoto: @aonanuga1956 (X) | Getty Image
Asali: UGC

Dalilin gina sola a fadar Aso Villa

Saboda haka ne Shugaba Bola Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 10 domin gina tashar wuta mai amfani da hasken rana a Villa, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zantawa da manema labarai ranar Juma'a, Mustapha ya ce wannan matakin na cikin shirye-shiryen Tinubu na bunƙasa hanyoyin samar da makamashi da rage kuɗin gudanarwa.

Ya ƙara da cewa tashar za ta ba da wutar lantarki mara yankewa kuma mai tsafta, samar da ayyukan yi, da bunƙasa ƙwarewar injiniyoyi da masana makamashi na Najeriya.

Haka kuma, ya bayyana cewa shirye-shiryen gwamnati na yanzu sun sanya masu zuba jari na ƙasashen waje ware $5.3bn domin saka jari a harkar wutar lantarki.

Matsalar wutar lantarki a Aso Villa

A cikin 2024, wata talla mai taken ‘Sanarwar yanke wuta’ daga kamfanin AEDC ta bayyana cewa ana bin fadar shugaban kasa bashin kudin wuta har Naira miliyan 923.87.

Kamfanin ya bai wa Aso Villa da wasu hukumomin gwamnati 86 gargadin kwanaki 10 su biya bashin Naira biliyan 47.1 ko a yanke musu wuta.

Sai dai shugaban ƙasa Tinubu ya hanzarta bada umarni na biyan bashin don kauce wa yanke wuta a babban ofishin mulki na ƙasar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce an cimma matsaya bayan tantance bayanan wutar da aka sha tsakanin kamfanin AEDC da fadar shugaban ƙasa.

Tinubu ya ba da umarnin a biya AEDC bashin kudin wutar da take bin fadar shugaban kasa
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

An ji ainihin bashin da AEDC ke bin Aso Villa

Sanarwar ta ce:

“Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta biyan kuɗin da ake bin Aso Villa ga kamfanin wutar lantarki naAEDC.
“A cewar wasiƙar AEDC zuwa ga babban sakataren fadar shugaban ƙasa a ranar 14 ga Fabrairu, 2024, AEDC na bin Aso Villa bashin ₦342,352,217.46, ba ₦923m ba.
“Bayan sulhu tsakanin ɓangarorin biyu, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Rt Hon. Femi Gbajabiamila, ya tabbatar da cewa za a biya kuɗin nan da ƙarshen mako.”

Onanuga ya ce shugaban ma’aikatan ya ja hankalin sauran ma’aikatu da su tantance asusunsu tare da AEDC, su kuma biya bashin wutar lantarki da ake bin su.

An shawarci 'yan Najeriya su koma kan sola

A zantawar Legit Hausa da wani kwararren mai hada sola, Gaddafi Muhammad daga jihar Kaduna, ya shawarci 'yan Najeriya da su yi kokari su koma amfani da sola.

A cewar Gaddafi:

"Yanzu da fadar shugaban kasa ke shirin komawa kan sola, wanne darasi ya kamata 'yan Najeriya su dauka? Su koma kan sola.
"Kowa ya san wutar Najeriya ba ta da tabbas, kuma dumamar yanayi na ci gaba da tsananta, za ka ga har lokacin sanyi ma ana zafi da rana.
"Wannan ya sa nake ganin akwai bukatar mutane su sanya sola a gidajensu, ko da wacce za ta dauki fanka, talabijin, da kwai."

Gaddafi ya ce ana fara hada sola ne daga N500,000 abin da ya yi sama, ya danganta da karfin mutum, amma ya ce:

"Yanzu batiri mai ruwa, mai karfin 220A, yana kai N300,000 sabo, amma ana samun na hannu a kan N170,000. Sai farantin hasken ranar, ana samun na hannu a kan N50,000 duk guda daya, wanda ake son akalla biyu.
"Sai kuma mutum ya sayi na'urar sauya hasken ranar zuwa lantarki, watau inbata, ita ma ta kai N160,000 mai kyau, sannan a yi maganar sauran kayayyakin hadin wanda zai iya kai wa N150,000, sai kudin aiki."

"Akwai sola a White House" - Gwamnati

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fadar shugaban ƙasa ta kare kudirin amfani da Naira biliyan 10 don girka na'urar wutar hasken rana a Aso Rock Villa.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan watsa labarai, Bayo Onanuga, ya kwatanta wannan shiri da tsarin makamancin sa da aka aiwatar a Fadar White House, Amurka.

Yayin da wasu ke ganin wannan shiri yana da amfani, wasu kuma na sukar kashe kuɗin bisa la'akari da matsin tattalin arziki da ake ciki a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.