Hajj 2022: Yadda alhazan Najeriya da na duniya su ka yi cincirindo a Dutsen Arfah

Hajj 2022: Yadda alhazan Najeriya da na duniya su ka yi cincirindo a Dutsen Arfah

  • A yau ne musulman duniya ke yin daya daga cikin manyan ibadu masu karfi, wato aikin Hajjin 2022
  • Ana tsayuwar Arafah, inda miliyoyin musulmai a fadin duniya suka taru kan dutsen da ke a kasar Saudiyya
  • Rahoton da muka samu ya ce, akalla mutane 42,000 ne daga Najeriya suka samu halartar wannan ibada

Arafah, Saudiyya - Sama da alhazai miliyan daya ne suka yi dafifi a Dutsen Arafah domin gudanar da aikin Hajjin 2022, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Tsayuwar ta tsawon yini a Arafat na daya daga cikin manyan abubuwan da ake gudanarwa a aikin Hajji bayan fara a ranar Alhamis din da ta gabata.

Yadda aka yi hawan Arafah
Hajj 2022: Yadda alhazan Najeriya da na duniya su ka yi cincirindo a Dutsen Arafah | Hoto: islamonline.net
Asali: UGC

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa tsayuwar Arafah muhimmin bangare ne na aikin Hajji domin wuri ne da Allah ke karban dukkan addu'o'in da mahajjata ke yi.

Kara karanta wannan

Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

Ana sa ran mahajjata za su yi amfani da ranar don yin addu'o'i ga kansu, iyalai, abokai, al'ummar musulmi da ma kasashensu, Premium Times ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dutsen Arafah kuma ana kiransa da Jabal ar-Rahmah, ma'ana dutsen rahama.

A rana ta tara na aikin Hajji, mahajjata sun tashi daga Mina zuwa Dutsen Arafah inda suke tsaye cikin tawassuli tare da yin addu'o'i da karatun Alqur'ani.

A nan ne Annabi Muhammadu SAW ya yi hudubarsa ta karshe ga musulmin da suka raka shi aikin Hajjin bankwana na karshen rayuwarsa.

Mutum bai da Hajji matukar bai yi tsayuwar ranar Arafah ba, kamar yadda addinin muslunci ya karantar.

Aikin Hajji, wanda daya ne daga cikin manyan ayyukan addini na shekara-shekara a duniya, an wajabta wa dukkan musulmi yinsa akalla sau daya a rayuwarsu idan suka samu dama.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu na babbar Sallah 2022

A bana, kasa da mahajjatan Najeriya 42,000 daga jihohi daban-daban ne suka halarci wannan taro na addini.

Hajj 2022: Ma'aikatar Hajji ta sanar da korar wasu manyan jami'ai a kamfanin aikin Hajji

A wani labarin, ma'aikatar aikin Hajji ta Saudiyya ta sanar da korar wani shugaba da wani babban jami'i a "daya daga cikin kamfanonin aikin Hajji" da ke gudanar da ayyukan hajjin bana.

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta ce an cire su ne saboda rashin samar da isassun kula ga alhazai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ruwaito a safiyar ranar Alhamis.

Ma'aikatar ta ce matakin ya biyo bayan hada kai da kwamitin gudanarwa na kamfanin da kuma lura da ma'aikatar ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel