Hajjin 2025: Mahajjata 43,000 Za Su Fara Tashi daga Najeriya zuwa Saudiyya

Hajjin 2025: Mahajjata 43,000 Za Su Fara Tashi daga Najeriya zuwa Saudiyya

  • NAHCON da shugabannin hukumar jin daɗin alhazai na jihohi sun cimma matsaya kan fara jigilar mahajjata ranar 9 ga Mayun 2025
  • Hukumar ta ware alhazai 43,000 zuwa kamfanonin jiragen sama huɗu da za su yi jigilar hajjin bana zuwa kasar Saudiyya mai tsarki
  • NAHCON ta ja kunnen jihohi da su guji rajistar mata masu juna biyu, tana mai cewa an tanadi cibiyoyin lafiya a Makka da Madina

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta gudanar da wani muhimmin taro da shugabannin hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi.

An gudanar da taron ne domin duba matakin da kowace jiha ta kai a shirye-shiryen hajjin shekarar 2025.

Hajji
Mahajjatan Najeriya za su fara tashi ranar 9 ga Mayu. Hoto: National Hajj Commission of Nigeria
Asali: Facebook

A sakon da hukumar NAHCON ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa a wata mai kamawa za a fara jigilar alhazai zuwa Saudiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya gudana ne a ranar Litinin, 22 ga Afrilu, 2025, karkashin Forum of States, inda aka tattauna kan tanadin takardun tafiya, rigakafi, jakunkuna da sauran shirye-shirye.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullah Saleh Usman, ya bayyana cewa ana dab da fara tafiya aikin hajji, don haka ya bukaci jihohi su bayar da rahoton shirin da suka yi.

Kamfanononin da za su yi jigilar aikin Hajji

Kwamishinan ayyukan NAHCON, Prince Anofiu Elegushi, ya ce kamfanin Air Peace zai dauki mahajjata 5,128 a jihohin da suka haɗa da Abia, Anambra, Akwa Ibom da sauransu.

Kamfanin FlyNas zai ɗauki mahajjata 12,506 daga FCT Abuja, Kebbi, Lagos, Osun, Sokoto da Zamfara.

Max Air kuwa zai ɗauki mahajjata 15,203 daga Bauchi, Kano, Katsina, da wasu jihohin Arewa, inda zai yi amfani da jirage biyu masu ɗaukar mutum 400 da 560.

NAHCON
NAHCON ta yi gargadi kan rajista wa mata masu juna biyu. Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

Kamfanin Umza zai jigilar mahajjata 10,163 daga Kaduna, Adamawa, Neja da wasu jihohi, tare da amfani da jiragen B747 da B777.

An sanya ranar fara tafiya aikin Hajji

A cewar NAHCON, jimillar mahajjatan bana da aka ware wa jirage sun kai 43,000, kuma za a kammala jigilar daga 9 zuwa 24 ga Mayu.

Bayan kammala aikin Hajji a Saudiyya, NAHCON ta ce an shirya fara dawowar mahajjata daga ƙasa mai tsarki daga 13 ga Yuni zuwa 2 ga Yuli.

Gargadi kan mata masu juna biyu

Kwamishinan tsare-tsare da bincike na NAHCON, Farfesa Abubakar Yagawal, ya bayyana cewa an tanadi cibiyoyin lafiya a Makka da Madina domin kula da mahajjata.

Ya ce an raba katunan rigakafi (Yellow Card) ga jihohi, tare da jan kunne ga hukumomin alhazai da su guji rajistar mata masu ciki, domin kiyaye lafiyarsu.

Shettima zai yi taro da jami'an NAHCON

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya gayyaci shugaban NAHCON taron gaggawa.

Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da taron ne tsakanin shugaban hukumar, jami'an NAHCON da Shettima.

Kwanaki kadan kafin kiran taron, Kashim Shettima ya gargadi Farfesa Abdullahi Sale Usman kan yanayin kula da ayyukan hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng