An Kaddamar da Gagarumin Samame domin yi wa 'Yan Bindiga Kwab Daya

An Kaddamar da Gagarumin Samame domin yi wa 'Yan Bindiga Kwab Daya

  • Rundunar Sojin Najeriya ta ƙaddamar da sabon gagarumin samame kan ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata laifi a Arewa maso Yamma
  • An fara Operation Clean Sweep IV ne ta hanyar haɗa hare-haren ƙasa da na sama domin tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda da katse hanyoyin zirga-zirgarsu
  • Rundunar ta ce sojoji sun tilasta wa ’yan ta’adda tserewa daga maboyarsu a Katsina, yayin da hare-haren sama suka hallaka da dama daga cikinsu a Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Katsina – Rundunar Haɗin Gwiwar Soji ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, ta ƙaddamar da sabon gagarumin samame kan ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata miyagun laifuka a yankin.

An sanya wa sabon samamen suna Operation Clean Sweep IV, inda ake haɗa ayyukan sojojin ƙasa da na sama domin tarwatsa hanyoyin ayyukan ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Dogo Gide: Sojoji sun samu nasarar cafke na kusa da jagoran 'yan ta'adda da miyagu 60

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Wasu daga cikin dakarun Najeriya da aka tura Kwara. Hoto: Kwara State Government
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwar Sojin, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Sojoji sun tarwatsa ’yan ta’adda

Danja ya ce dakarun Najeriya sun gudanar da aikin share yankuna ranar Laraba a kusa da wasu maboyar ’yan ta’adda da ake zargi da kasancewa a ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.

Ya ce samamen ya tilasta wa ’yan ta’addan barin matsugunansu tare da tserewa zuwa dazuzzukan da ke kewaye da yankin.

A jihar Zamfara kuma, rundunar Operation Fansan Yamma ta kai hare-hare kan wasu ’yan ta’adda da aka ce suna taruwa a kan babura a ƙaramar hukumar Anka.

Za a farmaki Lakurawa

Danja ya ce wani muhimmin abin da Operation Clean Sweep IV ta mayar da hankali a kai shi ne tarwatsa ƙungiyar ’yan ta’adda ta Lakurawa.

Ya ce rundunar za ta kuma hana ƙungiyoyin ’yan ta’adda kutsawa cikin Najeriya ko samun ƙarin ƙarfi daga yankunan kan iyaka.

Kara karanta wannan

Sojoji da jiragen yaƙi sun zafafa hare hare, sun rutsa yan bindiga ta sama da ƙasa a jihohi 2

A cewarsa, ’yan ta’addan na amfani da wasu yankunan kan iyaka wajen zirga-zirga, samar da kayan aiki da kafa maboyarsu.

Za a kai samame Neja

Sahara Reporters ta wallafa cewa Danja ya ce aikin sojojin zai kuma shafi yankunan da ke kusa da mashigar Kogin Neja da Gandun Dajin Kainji.

Ya ce manufar hakan ita ce hana ’yan ta’adda amfani da yankunan a matsayin wuraren kaddamar da hare-hare kan al’ummomin Arewa maso Yamma.

Sojojin Najeriya a Kwara
Karin sojojin da aka kai Kwara a daji. Hoto: Kwara State Government
Source: Facebook

Rundunar ta ce Operation Clean Sweep IV ta nuna aniyar sojoji na ci gaba da matsa wa ’yan ta’adda da masu aikata miyagun laifuffuka lamba a yankin.

Za a kara dakarun soji a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar Sojin Najeriya ta fara shirin kafa sabbin rundunoni guda huɗu domin faɗaɗa ƙarfin aikinta wajen yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙara yawan rundunonin sojin daga guda takwas zuwa 12, inda za a kafa hedikwatoci a Benue, Kwara da Taraba, tare da wata runduna a jihar Edo.

Matakin na zuwa ne tare da shirin ɗaukar sababbin jami’an soja 28,000 da inganta kayan aiki, dabarun sufuri da jin daɗin jami’an tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng