Hajjin Bana
Hukumar Jin Dadin Mahajjatan Kano ta sanya kuɗin kujerar Hajjin 2027 a N7m, tare da tsayar da 25 ga Agusta a matsayin ranar ƙarshe ta yin rajista ga maniyyata.
Gwamnatin Jigawa ta amince da mayar wa kowane maniyyacin jihar N53,853 daga cikin kuɗaɗen da suka yi saura bayan gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Gwamnatin Jigawa ta amince da rancen Naira biliyan 3.5 domin biyan kuɗin ajiyar Hajjin 2027 ga maniyyata 466 daga jihar tare da cika wa'adin NAHCON.
Jami'ar Ahmadu Bello da NAHCON sun ƙulla yarjejeniya domin ƙaddamar da digirin MBA na harkokin Hajji da Umrah, tare da inganta horo da gudanarwa.
NAHCON ta buƙaci masu niyyar Hajjin 2027 su fara biyan ajiyar Naira miliyan biyar, yayin da Kwara da Taraba suka sanya wa'adin kammala biyan kuɗi.
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, ta yi albishir da shirin mayar wa mahajjata wasu daga cikin kudin da suka biya.
An samu rahoton rasuwar daya daga cikin Alhazan Najeriya da ke kasa mai tsarki. Alhajin ya rasu ne bayan ya gamu da hatsarin mota a birnin Makkah.
Mata biyu daga mahajjata daga jihar Sokoto sun riga mu gidan gaskiya a Makkah bayan kammala aikin Hajjin 2026 cikin nasara, kamar yadda jami'ai suka tabbatar.
Kamfanin sufuri na Flynaa ya tabbatar da cewa za a fara debo yan Najeriya da suka sauke farali a kasa mai tsarki a 2026 zuwa gida Najeriya daga yau Laraba.
Hajjin Bana
Samu kari