An Sanya Lokacin da Maniyyata za Su Kammala Biyan Kudin Hajjin 2025 a Jihar Kwara
- Hukumar alhazai ta Kwara ta ce kudin Hajjin 2025 zai bambanta a shiyyoyi saboda bambancin nisan tafiya zuwa Saudiyya
- Ranar ƙarshe da hukumar ta tsayar domin biyan kuɗin Hajjin bana ita ce Janairu 31, 2025, kuma ta ce ba za ta tsawaita wa’adin ba
- Hukumar ta fara shirin samar da biza ga maniyyata daga ranar Fabrairu 25, inda aka ja hankalin alhazai su cika takardunsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kwara ta bukaci maniyyata aikin Hajjin bana su biya N8,457,685.59 kafin ranar Juma’a, 31 ga Janairun 2025.
Mataimakin sakataren yada labaran hukumar, Sanni Muhammed ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Asali: Facebook
Tsarin biyan kudin Hajjin 2025 na jihohi
A cikin sanarwar da Punch ta samu, Sanni Muhammed ya ruwaito Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, shugaban hukumar yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kudin aikin Hajji na 2025 zai bambanta a duk fadin Najeriya saboda bambance-bambancen tazarar tafiya zuwa Saudiyya, wanda ke shafar farashin man jiragen sama kai tsaye."
A wata hira ta kai tsaye da ya yi da gidan rediyon Gerin 95.5 FM da Diamond 88.7 FM, Alhaji Abdulkadir ya ce alhazan jihar Kwara za su biya N8,457,685.59.
Kwara: An sanya ranar karshe ta biyan kudin Hajji
Shugaban hukumar ya ce maniyyata daga Borno da Adamawa za su biya N8,327,125.59 yayin da maniyyatan Kudancin Najeriya za su biya N8,784,085.59.
Ya kara da cewa:
"Bambancin yana nuna dawainiyar jigilar maniyyata saboda nisan tafiya da kuma tabbatar da rarraba farashin daidai wadaidai da a fadin kasar."
Abdulsalam ya ja hankalin masu shirin tafiya cewa ranar ƙarshe ta biyan kudin aikin hajjin bana ita ce 31 ga watan Janairun 2025, kuma ba za a tsawaita wa’adin ba.
An fadi abin da zai jawo wa alhazai matsala
Shugaban ya ce dole ne a biya kudin ga NAHCON a kan lokaci don cika wa’adin da Saudiyya ta gindaya.
Ya kuma bayyana cewa za a fara sarrafa biza daga ranar 25 ga Fabrairu, yana gargadin cewa jinkiri zai iya kawo cikas ga tafiyar maniyyatan.
Babban jami’in gudanarwa na hukumar, Alhaji Olayinka Shuaib, ya bukaci alhazai su kammala biyan kuɗi da gabatar da fasfo nasu cikin lokaci.
An ba maniyyata Hajjin 2025 shawara
Hukumar ta jaddada muhimmancin bin wa’adin da aka tsayar don gujewa matsaloli yayin shirye-shiryen tafiya aikin Hajjn bana.
Hukumar ta shawarci masu sha’awar sauke farali a wannan shekarar su tuntubi ofishin hukumar jin daɗin alhazai na jihar Kwara don karin bayani.
An yi kira ga alhazai su tabbata sun kammala dukkan shirye-shiryen da ake buƙata domin samun nasarar tafiyar Hajjin 2025.
Gwamnati za ta ba alhazai kudin guzuri
A wani labarin, mun ruwaito cewa, maniyyatan Najeriya za su samu tallafin $500 na BTA, wanda ya kai kimanin N830,000 bisa farashin N1,660 kan kowace $1.

Kara karanta wannan
Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron
Shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman wanda ya bayyana hakan ya ce gwamnatin tarayya na kokarin rage wa alhazan 2025 nauyin kudin kujera.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng