Gwamna Ya Fadi Matsayarsa, Ya Bayyana Wanda Arewa za Ta Zaba a 2027

Gwamna Ya Fadi Matsayarsa, Ya Bayyana Wanda Arewa za Ta Zaba a 2027

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa Arewa za ta goyi bayan shugaban kasa Bola Tinubu domin ya zarce
  • Gwamnan ya yi Allah wadai da 'yan siyasar Arewa da ke kokarin rarraba jama'a kan batun shugabanci da sake zaben Bola Ahmed Tinbu
  • Ya bayyana cewa Arewa za ta kiyaye yarjejeniyar karba-karba da aka kulla don ba Kudu damar samar da shugaban kasa a 2027
  • Alhaji Abdullahi Sule ya bukaci al'ummarsa su hada kai da kaucewa duk wani abu da zai haifar da rarrabuwar kawuna a tsakaninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana matsayin Arewa a zaben 2027 duk da yadda ake samun sabani game da batun.

Gwamnan ya ce Arewa ta ci gaba da tsayawa kan yarjejeniyar da aka kulla na karba-karba tsakanin Arewa da Kudancin kasar nan.

Tinubu
Gwamnan Nasarawa ya ce za a sake zaben Tinubu a 2027 Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

AIT ta ruwaito cewa Gwamna Sule ya bayyana wannan ne yayin da yake yi wa taron bikin Nzeh Mada da aka gudanar a Karamar Hukumar Akwanga a jihar Nasarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule ya ce za a zabi Tinubu a 2027

Gwamna Abdullahi Sule ya sanar da masu sauraro cewa Arewa za ta goyi bayan shugaban kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu, domin sake koma wa kujerarsa a 2027.

Ya ce zai bayyana matsayarsa a kan 'yan siyasar Arewa da ke kalubalantar burin Tinubu na ci gaba da shugabanci a karo na biyu .

Abdullahi Sule ya kara da cewa, kamar yadda Arewa ta yi aiki tukuru wajen nasarar Tinubu a zaben 2023, haka kuma za a yi aiki tukuru wajen ganin an sake zaben shi a 2027.

Gwamnan Nasarawa ya caccaki masu sukar Tinubu

Gwamnan ya zargi wasu 'yan siyasa daga Arewa da kokarin rikita jama'a, inda ya dage da cewa Arewa dole ta kiyaye darajarta ta hanyar bin yarjejeniyar canjin mulki.

Sule ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga al'ummar Mada da su hada kai tare da kaucewa duk wani abu da zai iya haifar da rarrabuwar kawuna.

Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ya bukaci al'ummar su yaba da shugabanni da suka zo don kawo sauyi mai kyau da kawo ci gaban da ake bukata da kwanciyar hankali a yankunansu ba ku daya.

An shawarci Tinubu a kan neman takara

A baya, kun ji cewa tsohon mai ba wa mataimakin shugaban kasa shawara ya shawarci Bola Ahmed Tinubu a kan ya sake tunani a kan sake tsaya wa takara a 2027 mai zuwa.

A cikin bayanin da ya yi, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce ya gano kurakurai da dama a cikin yadda ake tafiyar da matsalolin da aka gada daga gwamnatin da ta gabata da ta yanzu.

Hakeem Baba-Ahmed ya kara da cewa kamata ya yi a ce dukkanin tsofaffin yan siyasa sun hakura da tsayawa takara, a kuma bar matasa su warwasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.