Ba Daidai Bane: Peter Obi Ya Tausayawa Dalibai kan Wahalar Rubuta JAMB
- Peter Obi ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda ake tursasa wa dalibai zuwa cibiyoyin jarrabawa da sassafe
- Obi ya koka kan yadda Najeriya ke da karancin yawan jami’o’i tare da bayyana yadda kasar ke bukatar gyara a fannin ilimi
- Najeriya na da akalla 200, wanda hakan ke bayyana barazana da kuma cunkoson dalibai a kasar mai mutane sama da miliyan 230
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Najeriya - Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana damuwa kan yadda ake tilasta wa dalibai, masu shekaru 15 zuwa 17, fita da sassafe domin rubuta jarabawar JAMB a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 27 ga Afrilu, Obi ya ce wannan tsari na sa wa yara jarabawa tun karfe 6:00 na safe abin kunya ne kuma barazana ce ga lafiyar su.
A cewarsa:
"Na samu rahotanni da dama na dalibai da ake bukatar su halarci jarrabawa da karfe 6:30 na safe. Wannan ba daidai bane a tilasta wa yara kanana tafiya cikin duhu da hadari saboda kawai suna neman hakkinsu na ilimi."

Asali: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni na nuna hadurra da bacewar dalibai
Obi ya bayyana cewa wasu dalibai suna shiga hatsari, wasu suna bacewa, yayin da wasu ke fuskantar matsanancin firgici da hadurra saboda irin wannan tsarin.
Ya kara da cewa:
"Wa zai dauki alhakin yarinya ko yaro dan shekaru 15 ko 16 da ya bace ko ya gamu da matsala yayin da yake kokarin neman ilimi?"
Ya ce wannan matsala ta fito da matsanancin gazawa a tsarin ilimi a Najeriya.
A ina matsalar take?
Obi ya ce Najeriya na da kasa da jami'o'i 200 kacal ga yawan jama’a da ya haura miliyan 230, yana nufin jami'a daya ga mutane miliyan daya, abin da ya kira "abin takaici."
Ya kuma bayyana cewa bisa bayanan Hukumar Ilimi ta Duniya (UNESCO) da IndexMundi, kasar da ke son ci gaba da bunkasa tattalin arziki na kokarin samun GER na kashi 40%.
Amma a Najeriya, Obi ya ce GER din bai wuce kashi 12% ba, wanda ya nuna rashin isasshen damar samun ilimi a kasa.
Obi ya kwatanta Najeriya da Indonesia
Obi ya kwatanta Najeriya da Indonesia, inda ya ce kasar Indonesia na da kusan jami'o'i 4,000 kuma tana da GER fiye da kashi 45%.
A cewar Obi:
"Idan Najeriya na da ko da rabi na irin jami’o’in da Indonesia ke da su — kusan 2,000 — da ba za a rika tilasta wa yara tafiya da dare domin rubuta jarabawa ba."
Ya kara da cewa, a Indonesia jami'o'i suna nan a ko'ina a fadin kasar, wanda ke saukaka damar karatu da kuma kare lafiyar dalibai.
Bukatar gaggawa na fadada ilimi a Najeriya
Peter Obi ya jaddada cewa bai kamata a dauki ilimi a matsayin wata alfarma ba, yana mai cewa ilimi shi ne babban ginshikin cigaban kowace kasa.
Da yake karfafa batunsa, y ace:
"Ba za ka ce kana son cigaba ba, alhali kana hana matasa samun ilimi. Ba za ka ce kana son mutanen ka ba, kana jefa yara cikin hadari lokacin jarabawa."
Ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta gaggauta fadada tsarin ilimi domin daidaitawa da karuwar yawan jama'a.
Asali: Legit.ng