Babu Rufa Rufa: An Bayyana Sunayen Mutane 3 da aka Kama da Bindiga a Filato
- Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta tabbatar da kama mutane uku da ake zargi da laifi a wani samame da aka kai a Jos ranar Litinin
- An cafke su ne bisa sahihan bayanan sirri da sashin sintiri na yankin Anglo Jos ya samu, inda aka gano bindiga kirar gida a hannunsu
- Nasarar kama mutanen na zuwa ne bayan jerin hare-hare da aka sha a jihar, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau - Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da cafke wasu mutum uku da ake zargi da laifi, tare da kwato bindiga kirar gida daga hannunsu a yayin wani samame.
An gudanar da kamen ne da misalin karfe 10:30 na dare ranar Litinin, 22 ga Afrilu, bayan samun sahihan bayanan sirri daga sashen sintiri na Anglo Jos.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kama mutanen ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafin shi na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamen ya biyo bayan tashin hankali da aka sha fama da shi a jihar, wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama a yankuna daban-daban.
Sunayen mutanen da aka kama a Filato
Rahotanni sun nuna cewa mutane ukun da aka kama su ne Michael Jimoh mai shekaru 26, Pam Davou mai shekaru 37, da Ibrahim Isuwa mai shekaru 35.
A yayin da jami’an suka gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin, an gano bindiga kirar gida dauke da harsashi a hannunsu.
Ko da yake ba a bayyana cikakken wurin da aka kama su ba, jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da cewa suna hannunsu yanzu haka, yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba.
'Yan sanda za su yi cikakken bincike
Kamen na zuwa ne a daidai lokacin da Jihar Filato ke ci gaba da fuskantar hare-hare daga bata-gari, wanda ke haddasa fargaba da asarar rayuka a tsakanin al’umma.
Hukumomin tsaro sun kara zage damtse don hana yaduwar tashe-tashen hankula da kuma dakile barazanar tsaro da ke addabar jihar.

Asali: Facebook
Rundunar ‘yan sanda ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano ko akwai wasu karin mutane da ke da alaka da wadannan da aka kama, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da su.
Dama dai shugaban kasa Bola Tinubu ya ba umarnin daukar mataki a kan kashe kashe da ake fama da su a Najeriya, musamman a lokacin da ya tafi hutu kasashen Turai.
Rikicin rashin tsaro a jihar
Jihar Filato na ci gaba da fuskantar rikice-rikice da suka daɗe suna addabar yankin, musamman tsakanin al’ummomin da ke fafatawa kan fili, bambancin addini da na kabila.
Wadannan rikice-rikice sun haifar da mummunan tasiri a rayuwar jama’a, inda daruruwan mutane ke rasa rayukansu, gidaje na ƙonewa, kuma dubban mutane sun zama ‘yan gudun hijira a cikin jiharsu.
Hare-haren da ke faruwa lokaci-lokaci sun haifar da tsoro da rashin kwanciyar hankali, inda mutane ke barin gidajensu da dare, makarantu da asibitoci na rufewa, kuma tattalin arziki ya tsaya cik a wasu yankuna.
Duk da kokarin hukumomin tsaro, harin baya-bayan nan da ya kai ga kama mutane uku da ake zargi da mallakar makami a Jos, ya sake nuna irin barazanar da jihar ke ciki.
Masu ruwa da tsaki na kira ga gwamnati da ta kafa ingantaccen tsarin sasanci da kwanciyar hankali, domin kawo karshen wannan bala’i.
Amma har yanzu, kalubale na tsaro da rashin amincewa tsakanin al’umma na hana ci gaba da zaman lafiya mai dorewa.
Wannan yanayi na rikici ya sanya Filato ta kasance cikin jerin jihohin da ke bukatar kulawa ta musamman daga gwamnati da kungiyoyin agaji.
Tsaro: Gwamnan Benue ya nemi taimako
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Benue Hyacinth Alia ya bukaci taimakon gwamnatin tarayya kan tsaro.
Gwamna Alia ya bayyana cewa ya yi iya kokarin shi wajen rage hare hare da ake kai wa jihar bayan karbar mulki a 2023.
A karkashin haka, ya bayyana cewa babu bukatar sanya dokar ta baci a jihar Benue domin a acewar shi, matsalar ba ta fi karfn shi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng