Najeriya Ta Yi Rashi, Tsohon Shugaban Majalisa Ya Bar Duniya

Najeriya Ta Yi Rashi, Tsohon Shugaban Majalisa Ya Bar Duniya

  • Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Plateau, Peter Ajang Azi, ya rasu a ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026
  • Iyalansa sun ce Azi ya rasu cikin kwanciyar hankali, yayin da aka ce za a sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba
  • Sanata Simon Lalong ya bayyana mutuwar tsohon kakakin a matsayin babban rashi ga iyalansa, mazabarsa da jihar Plateau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jos, jihar Plateau - Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya, Peter Ajang Azi, ya yi bankwana da duniya.

Peter Ajang Azi ya rasu ne a ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, kamar yadda iyalansa suka tabbatar.

An yi babban rashi a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

John Daniel Azi, wanda ya yi magana a madadin iyalan marigayin, ya ce tsohon kakakin ya “huta ya koma ga Ubangijinsa” a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Makinde ya yi tunani, ya ɗauki tsohon daraktan DSS daga Katsina mataimakinsa

“Cikin cikakken miƙa wuya ga nufin Allah Maɗaukaki, Iyalin Azi Ajang na sanar da rasuwar ɗansu, ɗan’uwansu kuma mahaifinsu, Peter Ajang Azi, tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Plateau,” in ji shi.

Iyalin sun ce za su sanar da shirye-shiryen jana’izar marigayin nan gaba.

Azi taba zama shugaban majalisar dokikin Plateau

Azi, wanda ya wakilci Jos North West, ya taɓa zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Plateau a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

An zaɓe shi a ranar 10 ga Yuni, 2015, bayan da shi da Istifanus Mwansat suka yi kunnen doki da ƙuri’u 12-12.

An bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba. Sai dai Azi ya yi nasara a rana ta biyu bayan Mwansat ya janye daga takarar.

Daga baya, ’yan majalisa 17 cikin 24 sun tsige shi daga mukaminsa a ranar 11 ga Yulin shekarar 2018.

Sanata Lalong ya yi jimamin rasuwar Azi

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Mai neman takarar gwamnan PDP a Gombe ya fice daga jam'iyyar

A halin da ake ciki, Sanata Simon Bako Lalong, wanda ke wakiltar mazabar Plateau South a Majalisar Dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Plateau, ya bayyana matuƙar jimami kan rasuwar tsohon kakakin.

Tsohon gwamnan na jihar Plateau ya yi ta'aziyyar ne wani dogon rubutu a shafinsa na Facebook ranar Alhamis.

Sanata Lalong ya bayyana rasuwar Azi a matsayin babban rashi mai raɗaɗi ga iyalansa, waɗanda ya wakilta, jihar Plateau da kuma al’ummar siyasa.

Peter Ajang Azi ya bar duniya
Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Plateau, Peter Ajang Azi Hoto: Sagacious Bello Lukman
Source: Facebook

Ya tuna da irin gudunmawar da Azi ya bayar wajen ci gaban jihar Plateau, musamman a lokacin da yake matsayin kakakin majalisar.

Lalong ya ce marigayin amintaccen abokin siyasa ne kuma ɗan jam’iyyar APC mai ƙwazo, wanda ya kasance mai kishin yi wa jama’a hidima, musamman a matakin ƙasa.

Tsohon sanatan Ondo ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Tsohon Sanatan da ya wakilci Ondo ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, Omololu Samuel Meroyi, ya rasu.

Majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun tabbatar da cewa marigayi tsohon sanatan ya bar duniya yana da shekara 76 a duniya.

An zaɓi Omololu Samuel Meroyi zuwa Majalisar Dattawa a shekarar 1999 a ƙarƙashin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD), inda ya wakilci mazabar Ondo ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng