An Samu Sauƙi bayan Kawo Ƙarshen Hatsabibin Ɗan Bindiga da Yaransa 10 a Katsina
- Wani fitaccen jagoran 'yan bindiga, Harisu Babba Yauni, ya mutu tare da wasu daga cikin yaransa a rikicin cikin gida da ya auku a dajin Yauni
- Lamarin ya faru ne da safiyar ranar 23 ga Afrilu, 2025, a karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina, a cewar jami'an tsaro
- An gano cewa wasu gungun 'yan bindiga daga Kambarau, Tudun Dole da dajin Mahuta suka kai masa farmaki suka hallaka shi da mabiyansa
- Babba Yauni na cikin wadanda ake zargi da kashe jami’in PMF a sansanin Zakka, wanda hakan ya janyo jami’an tsaro suka saka shi a gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - An sake rage mugun iri a jihar Katsina bayan mutuwar hatsabibin ɗan bindiga yayin arangama da wasu ƴan ta'adda a yankin.
An ce Harisu Babba Yauni, daya daga cikin manyan 'yan bindiga da aka sani da aikata mugayen laifuffuka, ya mutu.

Asali: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ya ce riƙakken ɗan ta'addan ya mutu tare da mutum 10 a dajin Yauni, Zakka da ke karamar hukumar Safana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Zamfara
Hakan ya biyo bayan kwanton bauna da rundunar Sojoji suka yi wanda ya hallaka Ibrahim Kaboni da wasu ‘yan bindiga a wajen garin Tsafe da ke jihar Zamfara.
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne a daren ranar 16 ga Afrilun shekarar 2025 yayin wani samame da dakarun Operation FANSAN YANMA ke yi a yankin.
An yi kwanton baunar hadin gwiwa da jami’an tsaro daban-daban wanda ya yi ajalinsa bayan sa ido na tsawon lokaci kan motsin ‘yan bindigar.
An ce Kaboni na cikin jerin masu laifi da ake nema ruwa a jallo a dalilin kai hare-hare, satar shanu da garkuwa da mutane a yankin.

Asali: Facebook
Yadda ɗan bindiga ya mutu yayin arangama
Jami’an tsaro sun tabbatar cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar 23 ga Afrilu, 2025, a jihar Katsina.
Majiyar jami'ar tsaron ta ce:
“An kai wa Babba Yauni da gungunsa hari ne daga wasu ‘yan bindiga na Kambarau, Tudun Dole da Kauyen Mahuta a yankin Tsaskiya."
Ana zargin Harisu Babba Yauni da kisan jami’in PMF a sansanin Zakka, wanda ya sa jami’an tsaro suka dade suna farautarsa.
Kisan rikakken ɗan bindigar ya sake kwantar wa mazauna yankunan hankali, suka ce hakan zai kara musu karfin guiwar taimakawa jami'an tsaro domin kakkabe miyagun.
'Yan bindiga sun hallaka limami a Katsina
A wani labari mai kama da wannan, kun ji cewa wasu yan bindiga sun yi barna a wani kauye da ake kira Tudun Malamai a jihar Katsina.
Maharan sun kai hari a lokacin sallar Isha a kauyen da ke karamar hukumar Faskari da daren jiya Laraba 23 ga watan Afrilun 2025.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sun harbe limamin da ke jagorantar sallar, hakan ya tayar da hankalin al'umma masu ibada a masallacin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng