Kakakin Fadar White House za Ta Ajiye wa Trump Aiki Ta Yi Gaba
- Kakakin Fadar White House, Karoline Leavitt, za ta bar mukaminta a ƙarshen watan Agusta domin ta mayar da hankali kan yaranta da iyalinta
- Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana Leavitt a matsayin ɗaya daga cikin manyan mataimakansa da ya fi amincewa da su
- Leavitt mai shekaru 28 ta zama mafi ƙarancin shekaru da ta taɓa riƙe mukamin kakakin Fadar White House, kuma ba a bayyana wanda zai maye gurbinta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington, DC – Kakakin Fadar White House, Karoline Leavitt, za ta sauka daga mukaminta a ƙarshen watan Agustan 2026 kamar yadda Shugaba Donald Trump ya sanar.
Trump ya ce Leavitt, wadda ya kira ɗaya daga cikin "mataimakansa da ya fi amincewa da su", za ta bar aikin domin ta samu ƙarin lokacin kula da ƙananan yaranta.

Source: Twitter
Donald Trump ya yabawa Karoline Leavitt
BBC ta wallafa cewa Trump ya bayyana cewa zai ci gaba da amfanuwa da ƙwarewar Leavitt bayan ta bar Fadar White House.
Ya ce:
"Karoline yanzu za ta kasance ɗaya daga cikin manyan mashawartana daga waje, kuma za ta kasance murya mai tasiri a cikin Jam'iyyar Republican."
Leavitt mai shekaru 28 ta fara riƙe mukamin kakakin Fadar White House a bara, inda ta kafa tarihi a matsayin mafi ƙarancin shekaru da ta taɓa riƙe wannan matsayi.
Dai dai rahotanni da suka fito sun nuna cewa har yanzu ba a bayyana wanda zai maye gurbinta ba a karshen wannan watan.
Leavitt ta bayyana dalilin barin aiki
Rahoton Al-Jazeera ya ce Leavitt ta haifi ɗanta na biyu, mace, tare da mijinta Nicholas Riccio a watan Mayun shekarar 2026.
Tana kuma da ɗa mai shekaru biyu, kuma ta koma bakin aiki a watan da ya gabata bayan hutun haihuwa.
Bayan sanarwar Trump, Leavitt tabayyana cewa aikin ya kasance abin alfahari a gare ta kuma ta yi godiya a kan damar da aka ba ta.
Ta ce kasancewa uwa tare da kula da sabon jariri yayin aiki a ɗaya daga cikin ayyukan da suka fi wahala a duniya ya kasance lokaci mai cike da ƙalubale da kuma farin ciki.

Source: Getty Images
Leavitt ta ce bayan ta koma Fadar White House bayan haihuwar 'yarta, ta fahimci cewa ba za ta iya zama uwa mafi nagarta ga yaranta biyu ba tare da rage lokacin da take bai wa aikinta.
Ta ce hakan ne ya sa ta yanke shawarar barin Fadar White House domin fara wani sabon babi a rayuwarta.
Trump ya sauya jirgi a asirce
A wani labarin, mun ruwaito cewa Donald Trump ya sauya jirgin saman da yake ciki a asirce bayan ya halarci taron NATO a Turkiyya a watan da ya gabata.
Rahotanni sun ce Trump ya fara shiga tsohon jirgin Air Force One a gaban kyamarorin talabijin, kafin a ɓoye shi zuwa wani ƙaramin jirgin soji ta hanyar amfani da motar ɗaukar abinci.
An ce wasu 'yan jarida da ma'aikatan Fadar White House da ke cikin jirgin ba su san cewa an fitar da Trump a ɓoye ba, bayan jami'an Amurka sun gano wata barazanar Iran da ake zargin za ta iya kai hari kan jirgin.
Asali: Legit.ng

