Kisan Bayin Allah Sama da 100 a Filato Ya Harzuƙa Jama'a, An Ɓarke da Zanga Zanga

Kisan Bayin Allah Sama da 100 a Filato Ya Harzuƙa Jama'a, An Ɓarke da Zanga Zanga

  • Zanga-zanga ta ɓarke a Jos, babban birnin jihar Filato ranar Litinin sakamakon karuwar hare-haren ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne
  • Daruruwan mutane sun fito zanga-zangar ne kan kashe-kashen da ya ki ci ya ƙi cinyewa domin nuna ɓacin ransu da jawo hankalin gwamnati
  • Wasu rahotanni da ake yaɗawa a baya bayan nan sun nuna cewa an yi asarar rayuka sama da 100 a hare-haren kwanan nan a jihar Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau - Mutane da galibi Kiristoci ne sun ɓarke da zanga-zanga a Jos, babban birnin jihar Filato da ke Arewa maso Tsakiya yau Litinin, 21 ga watan Afrilu, 2205.

Zanga-zangar ta ɓarke ne sakamakon hare-haren da ake ci gaba kai wa kan al'umma wanda ya jawo asarar gomman rayuka a Filato.

Zanga zanga.
Zanga-zanga ta barke a Jos kan kashe kashen da ake ci gaba da yi a Filato Hoto: @Nwaadaz
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta tattaro cewa ana zargin fulani makiyaya ke aikata wannan kashe-kashen wanda ya jawo hankulan manyan ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki Tinubu ya ɗauka a Filato?

Idan ba ku manta ba, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tir da abubuwan da ke faruwa a Filato, inda ya umarci hukumomin tsaro su gaggauta magance lamarin.

Ya kuma umarci Gwamna Caleb Mutfwang ya shiga tsakani domin kawo ƙarshen asarar rayukan fararen hula.

Rahotanni sun bayyana akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da ƴan bindiga suka kai yankin ƙaramar hukumar Bokkos a baya-bayan nan.

Kashe-kashen Filato ya harzuƙa mutane

Wannan ne ya jawo mutane suka fito kan tituna yau Litinin domin nuna damuwarsu kan wannan hare-hare da ake ci gaba da kai wa.

Zanga-zangar na gudana ne karkashin jagorancin shugabannin Kiristoci ciki har da shugaban kungiyar CAN na jihar Filato, Rabaran Polycarp Lubo.

An tattaro cewa masu zanga-zangar sun fara ne daga titin Fwavwei Junction, inda suka haddasa cunkoso mai tsanani da jefa matafiya cikin kunci.

Wannan zanga-zangar ta zo ne kwanaki bayan rahotanni sun fara yawo cewa waɗanda aka kashe sun haura mutane 100 a kananan hukumomin Bokkos da Bassa cikin makonni biyu da suka gabata.

Zanga zanga.
Masu zanga zanga sun toshe tituna a Jos Hoto: @Nwaadaz
Asali: Twitter

Abin da masu zanga-zanga ke buƙata

Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Gyang Dalyop, ya bayyana cewa:

"Ba mu jin daɗin ci gaba da kai hare-hare da kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi a garuruwanmu. Wannan ne yasa muka sake fitowa domin nuna bacin ranmu.”

Haka zalika, wata mace daga cikin masu zanga-zanga, Hannatu Philip, ta bukaci gwamnati da ta gaggauta daukar mataki kafin lamarin ya sha ƙarfinta, rahoton The Cable.

Masu zanga-zangar dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban sun dunguma zuwa Gidan Gwamnatin domin mika bukatunsu na samar da tsaro cikin gaggawa.

Sojoji sun daƙile harin ɗaukar fansa

A baya kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya suj daƙile yunƙurin kai harin ɗaukar fansa a yankin ƙaramar hukuƙar Bassa ta jihar Filato.

Sojojin sun kai ɗauki ne bayan sanun rahoton cewa an sanya wa wasu shanu 32 mallakin wani makiyayi guba kuma duk sun mutu.

Majiyoyin sojoji sun ce makiyayin ya lura da canji a lafiyar dabbobinsa, abin da ya sa ya zargi an ba su guba a abincin da suka ci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262