'Yan Bindiga Sun Bindige Limami Yana tsaka da Jagorantar Sallar Ishai a Katsina

'Yan Bindiga Sun Bindige Limami Yana tsaka da Jagorantar Sallar Ishai a Katsina

  • 'Yan bindiga sun kai hari a lokacin sallar Isha a Tudun Malamai, karamar hukumar Faskari, Jihar Katsina da daren jiya Laraba 23 ga watan Afrilun 2025
  • An tabbatar da cewa sun harbe limamin da ke jagorantar sallar, lamarin da ya tayar da hankalin al'umma masu ibada a masallacin da ke kauyen Tudun Malamai
  • A cewar mazauna yankin, mutane biyu sun jikkata sakamakon harin yayin da maharan suka yi awon gaba da mutum akalla 10 wanda ya daga hankulan mutane
  • Har yanzu ba a san inda aka kai wadanda aka sace ba, yayin da 'yan sanda ke ci gaba da bincike da kokarin ceto su da kuma cafke masu hannu a shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Faskari, Katsina - Ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari a daren jiya Laraba 23 ga watan Afrilun 2025 a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

Ƴan bindigar sun kai hari kan masu ibada yayin sallar Isha a Tudun Malamai da ke karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina a daren ranar Laraba.

Yan bindiga sun kai hari kan masu salla a Katsina
'Yan bindiga sun yi ajalin limami da ke jagorantar salla a Katsina. Hoto: Legit.
Asali: Original

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Bakatsine ya wallafa a manhajar X a yau Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025 da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya fusata da kashe-kashen al'umma

Wannan na zuwa ne bayan ganawar Bola Tinubu da Nuhu Ribadu da kuma sauran shugabannin tsaro kan kashe-kashen al'umma a Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro su sauya dabarunsu nan take domin kawo karshen tashin hankali musamman a jihohin Borno, Benue da Plateau.

Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro na tsawon sa'o’i biyu a Abuja, inda nuna damuwa kan abin da ke faruwa tare da cewa kashe fararen hula ya isa haka.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce Tinubu ya bukaci hadin gwiwa da kananan hukumomi da gwamnonin jihohi don yakar matsalolin tsaro cikin al’umma.

Tinubu ya gana da Ribadu da shugabannin tsaro
Bola Tinubu ya umarci Ribadu da shugabannin tsaro kan kawo karshen yan bindiga. Hoto: @aonanuga1956.
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun hallaka limami a Katsina

Rahotanni sun ce an kashe limamin da ke jagorantar sallar a lokacin harin, lamarin da ya bar jama'ar yankin cikin firgici da tashin hankali.

Haka nan, maharan sun jikkata mutane biyu a yayin harin, wanda ya faru a cikin masallaci ana tsaka da ibada da daren jiya Laraba 23 ga watan Afrilun 2025.

Sun kuma sace akalla mutane 10 daga cikin masu sallah, lamarin da ya bar dangi da makwabta cikin kuka da fargaba.

Sokoto: Shugaban karamar hukuma ya sha kyar

A baya, kun ji cewa wasu yan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a ƙauyen Kalanjeni da ke ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.

An tabbatar da cewa an kai harin a ranar Laraba 23 ga watan Afrilun 2025, ya kusa ritsawa da shugaban ƙaramar hukumar, Isa Kalanjeni da ke jihar.

Bayan sun kasa cimma Isa Kalanjeni, ƴan bindigan sun sauke fushinsu a kan mutanen ƙauyen inda suka yi ɓarna mai tarin yawa wanda ya hargitsa al'ummar yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.