Gwamnatin Najeriya Ta ba da Hutun Kwanaki 2 domin Bukukuwan Kiristoci
- Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Juma’a, 18 da Litinin, 21 ga Afrilu, 2025, a matsayin ranakun hutu domin bikin Good Friday da Easter Monday
- Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da lokacin wajen yin tunani kan soyayyar da Yesu Almasihu ya nuna
- Tunji-Ojo ya kuma jaddada cewa gwamnatin Bola Tinubu na ci gaba da aiwatar da shirin “Renewed Hope” don samar da cigaban kasa mai dorewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun Juma’a da Litinin, 18 da 21 ga Afrilu, 2025, a matsayin ranakun hutun bikin Easter da Good Friday.
Hakan zai sanya rufe ma'aikatu a ranakun domin samun damar yin bikin da Kiristoci ke gudanarwa duk shekara.

Asali: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan hutun da gwamnatin Najeriya ta bayar ne a wani sako da ma'aikatar cikin gida ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta fito ne daga bakin ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, a madadin gwamnatin tarayya, inda ya mika sakon taya murna ga dukkan Kiristoci a fadin Najeriya.
Babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani ta bukaci ‘yan kasa da su dauki lokacin bikin a matsayin dama don yin aiki da darasin sadaukarwa da soyayya da Yesu Kiristi ya koyar.
An bukaci yin addu'a a lokacin Easter
Minista Tunji-Ojo ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin hutun wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a kasar nan.
Ya jaddada cewa Najeriya na bukatar hadin kan jama’a a kowane lokaci musamman a irin wannan lokaci da ake bukatar sada zumunci da rungumar juna ba tare da bambanci ba.
Ma'aikatar yada labarai ta wallafa cewa Tunji-Ojo ya ce:
“Ya kamata mu yi amfani da wannan dama wajen tunawa da darasin sadaukarwa da soyayya, da kuma yin addu’a ga cigaban kasa.”
Tunji-Ojo ya fadi kokarin da Tinubu ke yi
Ministan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Bola Tinubu na ci gaba da aiwatar da tsare tsare karkashi manufar “Renewed Hope” wanda ke da nufin tabbatar da cigaban kasa mai dorewa.
Ya kara da cewa gwamnatin na kokarin ganin an cimma nasara a fannonin tattalin arziki, tsaro da jin dadin jama’a.

Asali: Facebook
A karshe, ministan ya yi fatan Kiristoci za su yi murnar Easter cikin farin ciki da lumana, tare da fatan alheri ga daukacin ‘yan Najeriya a wannan lokaci na musamman.
Legit ta tattauna da Jacinta
Wata mabiyar addinin Kirista a jihar Kaduna, Jacinta Lona ta bayyana wa Legit cewa za ta yi amfani da lokacin Easter wajen yi wa kasa addu'a.
Jacinta ta ce:
"Dama muna yi wa kasa addu'a, kuma kamar yadda shugabanni suka bukata, za mu cigaba da yi a wannan lokacin ma.
"Sai dai akwai bukatar shugabanni su dage wajen magance matsalolin Najeriya kamar yadda suke bukata a rika yin addu'a."
An bukaci inganta tsaron cikin gida
A wani rahoton, kun ji cewa kun ji cewa lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Audu Bulama Bukarti ya yi magana kan yadda tsaro ke kara lalacewa.
Audu Bulama Bukarti ya ce a halin yanzu 'yan Boko Haram na cin karensu babu babbaka ta inda suke yada manufofinsu a kafafen sada zumunta musamman TikTok.
Barista Bukarti ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta dauki matakin rufe akawun din 'yan ta'addan ko da ba za ta iya bin diddiginsu ta kama su ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng