Hare-haren makiyaya a Najeriya
Wasu gungun 'yan bindiga sun kai sabon hari jihar Kaduna, inda suka sace shanu 365 a garuruwan Fulani 4. An roki gwamnati da hukumomin tsaro su kai dauki.
Rundunar 'yan sanda jihar Bauchi ta kama mutum shida a wani fada da aka gwabza tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Zaki. An kashe mutum daya.
'Yan majalisar wakilai sun yi muhawara game da karuwar hare-haren 'yan bindiga a fadin Najeriya. Sun bukaci kare iyakokin bayan kai hare-hare 24,000 a shekara.
Kungiyar MACBAN ta roƙi Shugaba Donald Trump da Majalisar Dokokin Amurka su cire sunanta daga duk wani jerin sunaye da ke danganta ta da ta’addanci a Najeriya.
Gwamnatin jihar Gombe ta dakatar da sarakunan gargajiya kan manoma da makiyaya a karamar hukumar Funakaye. Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane.
Wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Benue ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3. Har yanzu ana neman mutum daya da ba a same shi ba.
'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a Filato, a wasu hare-haren ramuwar gayya, lamarin da ya tilasta gwamnati ta daukar matakan tsaro na gaggawa.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kan makiyaya a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun hallaka wani makiyayi tare da kashe shanu masu yawa da sace wasu.
Ana fargabar makiyaya sun kashe mutane 9 ciki har da dan sanda a Benue, yayin da matsalar tituna ke hana jami’an tsaro isa cikin gaggawa domin ceto rayuka.
Hare-haren makiyaya a Najeriya
Samu kari