
Fulani Makiyaya







Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kafa ma'aikatar kiwo domin magance matsala da rikicin manoma da makiyaya da bunkasa tattalin jihar a Itas Gadau.

A cikin shekara biyar da suka gabata an kashe shugabannin kungiyar Miyetti Allah guda bakwai a sassan daban-dabna na Najeriya. Legit Hausa ta jero muku sunayensu.

An samu tashin hankali bayan barkewar fadan Fulani da Manoma a jihar Jigawa. Mutane sun riga mu gidan gaskiya yayin da aka raunata wasu mutum hudu.

Shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo ya shigar da kara kan tsare shi da aka yi ba tare da gurfanarwa ba. An kama shi bayan rikici tsakanin Fulani da tsohon soja.

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci a saki shugaban Miyetti Allah, Beloo Badejo da gaggawa. Majalisar ta bukaci Hafsun tsaro ya gurfana a gabanta.

Ana fargabar rasa rayukan mutane biyu yayin da rahotanni suka tabbatar da rikici tsakanin makiyaya da manoma a karamar hukumar Billiri da ka jihar Gombe.

Dangin Bello Bodejo sun yi kira ga sojoji da su gaggauta sako shi tare da ba da dama ga lauyoyi su gan shi, suna neman adalci kan lamarin Tudun Wada.

An samu tashin hankali tsakanin matasa da makiyaya a jihar Gombe. Rikicin wanda ya auku ya jawo sanadiyyar rasa rai yayin da wasu mutane suka jikkata.

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya sake bude kasuwar dabbobi ta Kara da ke a Birnin Gwari bayan shekaru 10 tana rufe. Ya ce za a mayar da wuta da sadarwa a yankin.
Fulani Makiyaya
Samu kari