"Ba Abu ne Mai Sauki ba"; Gwamna Abba Ya Fadi Wahalar Mulkin Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce mulkin Kano ba abu ne mai sauki ba saboda wasu dalilai da ya ambato
- Gwamnatin Kano ta ce ta horas da matasa kusan 2,000 karkashin Neighbourhood Watch domin tallafa wa jami’an tsaro a kananan hukumomi 44
- Wani masani ya bukaci gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma su hada kai wajen yaki da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce mulkin jihar ba abu ne mai sauki ba, yana mai bayyana Kano a matsayin “karamar Najeriya”.
Gwamna Abba ya ce mulkin na Kano bai da sauki saboda yawan al’ummarta da kuma kasancewarta jiha mai cike da mutane daga sassa daban-daban.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne ta hannun kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ambasada Ibrahim Waiya, wanda ya wakilce shi a taron farko na shekara-shekara kan tsaro na Institute of Security and Strategic Studies (ISSS).

Kara karanta wannan
Mataimakin gwamna ya kawo ruɗani, ya ce yan bindiga sun kai hare hare ƙananan hukumomi 26
A yayin taron, an karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf da lambar yabo ta ƙwarewa wajen tafiyar da harkokin tsaro.
Gwamnatin Kano ta dauki matakan tsaro
Bayan karbar lambar yabon, Waiya ya ce karramawar ta zama kira ga gwamnati da ta kara mayar da hankali kan tafiyar da harkokin tsaro.
Ya ce gwamnatin jihar ta rungumi hanyoyin yaki da rashin tsaro da suka hada da matakan amfani da karfi da kuma wadanda ba su shafi amfani da karfi ba.
A cewarsa, gwamnatin ta horas da matasa maza da mata kusan 2,000 karkashin shirin Neighbourhood Watch, sannan ta tura su zuwa kananan hukumomi 44 domin tallafa wa hukumomin tsaro na yau da kullum.
Waiya ya kuma bayyana ayyukan Anti-Phone Snatching Corps da shirin Safe Corridor a matsayin wasu daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka.
Ya ce an tsara shirin Safe Corridor ne domin karfafa wa matasan da ke shiga harkar daba da tashe-tashen hankula na siyasa gwiwar mika wuya da rungumar zaman lafiya.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu na neman 'ƙaryata' rahoton da ƙasar Amurka ta fitar kan Najeriya
A cewarsa, an yi wa matasa maza kusan 340 rajista tare da tantance su karkashin shirin, yayin da gwamnatin ta fitar da sama da N500m domin gudanar da shirin.
Abba ya bayyana kalubalen Kano
Abba Kabir Yusuf ya ce mulkin Kano na da matukar wahala saboda yawan al’ummarta da kuma yadda take hada mutane daga sassa daban-daban na Najeriya.
“Daya daga cikin masu magana a taron ya fada daidai cewa mulki ba abu ne mai sauki ba. Ba aikin malalaci ba ne saboda a zahiri kana mulkin jiha ce da take kamar karamar Najeriya."
“Kano tana da al’umma mai yawa sosai, kuma kwanan nan an bayyana ta cikin biranen da suka fi yawan al’umma a duniya. Jiha ce mai cike da mutane daga sassa daban-daban, domin mutane daga dukkan sassan Najeriya suna zaune a Kano."
“Saboda haka, Kano karamar Najeriya ce, kuma mulkinta ba abu ne mai sauki ba,” in ji shi.

Source: Facebook
Shugaba a Kwankwasiyya ya gana da Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya ta ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano, Alhaji Abdulaziz Gidanruwa, ya ziyarci Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gidanruwa na daga cikin mutanen da ake bayyana cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen ɗaukar nauyin NDC da kuma ƙungiyar Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar Nassarawa.
Asali: Legit.ng