Osun 2026: Dan Takarar Mataimakin Gwamna na APC Ya Sha da Kyar a Rumfarsa
- Mataimakin ɗan takarar gwamnan APC, Kayode Adereti, ya samu ya yi nasara da kyar da kuri'unƙuri’u 132 a rumfarsa a zaben Osun
- Jam'iyyar APC ta yi gagarumar nasara a rumfar tsohon Gwamnan Osun kuma sakataren ADC na kasa, Rauf Aregbesola, da ƙuri’u 256
- Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan Osun da aka gudanar yau Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Osun na jam’iyyar APC, Injiniya Kayode Adereti, ya sha da kyar a sakamakon zaben rumfarsa, inda ya samu nasara da tazarar ƙuri’u shida kacal.
Adereti, wanda ya jefa ƙuri’arsa a Ward 03, Unit 011, Ilare, a ƙaramar hukumar Ife Central, ya samu ƙuri’u 132 na APC, yayin da jam’iyyar Accord ta samu ƙuri’u 126.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Gwamna ya gano shirin da APC ta yi wajen tattara sakamakon zaben Osun

Source: Facebook
Jaridar Guardian ta tataro cewa ADC ta samu ƙuri’u 11, jimillar ƙuri’u 282 aka kaɗa a rumfar, yayin da aka ayyana ƙuri’u tara a matsayin marasa inganci.
Sakamakon ya nuna cewa an yi fafatawa sosai tsakanin APC da Accord a rumfar mataimakin ɗan takarar gwamnan na APC.
APC ta yi nasara a rumfar Aregbesola
Tsohon Gwamnan Jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya gamu da koma baya a siyasance a rumfarsa da ke Ilesa, bayan APC ta samu gagarumar nasara, cewar The Nation.
Aregbesola, wand shi ne sakataren ADC na kasa ya sha kaye a rimfar zabensa, inda APC ta samu ƙuri’u 256, ta zama jam’iyyar da ta yi nasara a rumfar, yayin da Accord ta samu ƙuri’u 43. ADC ta zo ta uku da ƙuri’u 13.
Sakamakon ya kasance mai muhimmanci saboda irin tasirin Aregbesola a siyasar jihar, kasancewarsa tsohon gwamna kuma ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasa a Ijesaland.
ADC ta sha kaye a rumfar Aregbesola
Tazarar ƙuri’u 213 da APC ta samu a kan Accord na nuna irin gagarumar nasarar da jam’iyyar ta samu a rumfar, inda ƙuri’unta 256 suka zarce jimillar ƙuri’un Accord da ADC.

Source: Facebook
Sakamakon zaben rumfar Aregbesola na daga cikin sakamakon da ake sa ran za a sanya ido a kansu tare da sauran rumfunan zaɓe a Ilesa da Ijesaland, yankin da ake ganin yana da tasiri.
Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar yau Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026, inda ake sa ran sanin wanda ya samu nasara nan ba da dadewa ba.
INEC ta fara dora sakamako a IReV
A wani labarin, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta far dora sakamakon zaben gwamnan jihar Osun a shafinta na yanar gizo (IReV).
Rahotanni sun nuna cewa INEC ta dora sakamakon rumfunan zabe 1,517 daga cikin jimillar 3,763, watau kashi 40.31 cikin ɗari.
Wannan ci gaba ya nuna fara tura sakamakon rumfunan zaɓe ta hanyar na’ura tare da bai wa jama’a damar kallon sakamakon yayin da jami’an zaɓe ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.
Asali: Legit.ng
