An Gano Gawarwaki 13 Cikin Mutane 200 da Jirgi Ya Kife Dasu a Kebbi

An Gano Gawarwaki 13 Cikin Mutane 200 da Jirgi Ya Kife Dasu a Kebbi

- An samu labarin cewa, cikin mutane kusan 200 da suka nutse a hadarin jirgin ruwan Kebbi, an gano gawarwaki 13

- Rahoton wata majiya ya bayyana cewa, an ceto wasu mutane 20 yayin da wasu masu aikin ceto suka yi aikin ceto

- An ce jirgin ya dauko kayan da ya fi karfinsa ne, wannan yasa aka samu barakar da ya jawo kifewarsa

Rahotanni sun bayyana cewa, an gano karin gawarwaki 13 daga cikin fasinjojin jirgin ruwan da ya kife a Jihar Kebbi.

Tun a ranar Laraba aka gano gawarwaki biyar bayan hatsarin jirgin da ke dauke da kusan mutum 200 daga Jihar Kebbi zuwa Neja.

Jirgin ruwan ya kife ne a yankin Tsohuwan Labata da ke Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi, bayan sa’o’i da fara tafiyar.

KU KARANTA: Ban Ji Dadi Ba: Shugaba Buhari Ya Shiga Jimamin Kifewar Jirgin Ruwa a Kebbi

An Gano Gawarwaki 13 Cikin Mutane 200 da Jirgi Ya Kife Dasu a Kebbi
An Gano Gawarwaki 13 Cikin Mutane 200 da Jirgi Ya Kife Dasu a Kebbi Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Wani mazaunin kauyen Warra, Adamu Umar Warra, ya shaida wa wakilin Aminiya ta waya cewa ana sa ran masu aikin ceto za su gano karin gawarwaki.

Manajan yankin na National Inland Waterways Authority (NIWA) a Yauri, Yusuf Birma, ya shaida wa manema labarai cewa hatsarin ya afku ne saboda lodin da ya fi karfin jirgin, ya kara da cewa an gano gawarwaki hudu.

Jami’in ya ce an ceto mutane 20 “kuma mutane 156 da suka bata ana fargabar sun mutu”.

Jirgin ruwan kuma na dauke da babura kirar Bajaj 30, in ji Mista Birma, Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Raba Kaduna Gida Biyu: Arewaci da Kudancin Kaduna Sun Amince Su Yi Hannun Riga

A wani labarin, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Sama’ila Dikko, ya ce dole ne Fulani makiyaya da ke shigowa jihar ta Kano su samu izini daga rundunar 'yan sanda ta jihar da za su baro zuwa Kano.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron gaggawa na tsaro tare da shugabannin hukumomin tsaro a ofishinsa a ranar Laraba, Mista Dikko ya ce duk wani Bafulatani makiyayi da ya shigo Kano ba tare da izinin ba za a mai dashi in da ya fito, in ji Daily Nigerian.

Ya ce wannan shawarar na daga cikin tsare-tsaren tsaro da rundunarsa ta yi a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel