Tirkashi: Lauyoyin Najeriya Sun Kawo Dokokin da Suka Hana Tinubu Dakatar da Fubara
- Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta soki dokar ta-bacin da shugaba Bola Tinubu ya ayyana a jihar Ribas, tana mai cewa hakan saba doka
- NBA ta jaddada cewa sashe na 305 na kundin tsarin mulki bai ba shugaban kasa ikon dakatar da zababbun shugabanni da 'yan majalisa ba
- Kungiyar ta nemi a bi hanyoyin doka da wajen warware rikicin siyasa, tare da gargadin cewa matakin Tinubu barazana ne ga dimokuradiyya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-baci da shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Ribas.
Shugaban kungiyar, Mazi Afam Osigwe, SAN, ya bayyana matakin da Tinubu ya dauka a matsayin saba doka da murkushe dimokuradiyya.

Asali: Twitter
Mazi Afam Osigwe ya bayyana matsayar kungiyar NBA ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar 18 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NBA ta ce Bola Tinubu ya sabawa doka
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa hauhawar tashin hankalin siyasa da lalata bututun mai ne suka sa aka ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas.
Sai dai NBA ta dage cewa sashe na 305 na kundin tsarin mulki na 1999 bai bai wa shugaban kasa ikon dakatar da gwamna ko ‘yan majalisa ba.
Kungiyar ta jaddada cewa dokar ta-baci ba ta bai wa shugaban kasa ikon cire gwamna, mataimakinsa, ko ‘yan majalisar jiha daga mukamansu ba.
Ta kara da cewa kundin tsarin mulki ya tanadi hanyoyi bayyanannu na sauke shugabanni da aka zaba, amma babu daya daga cikinsu da aka bi.
Lauyoyi sun kawo dokar ayyana dokar ta baci
NBA ta yi gargadin cewa an sauke Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, da ‘yan majalisa ba bisa ka’ida ba, kuma hakan barazana ce ga dimokuradiyya.
Kungiyar ta ce sabani na siyasa da rikicin majalisa ba su isa su zama hujjar dakatar da zababbiyar gwamnatin jiha ta hanyar dokar ta-baci ba.
NBA ta bukaci a bi hanyoyin doka da tsarin mulki don magance irin wadannan matsaloli, maimakon katsalandan daga bangaren zartarwa.
Kungiyar ta jaddada cewa sashe na 305(2) na kundin tsarin mulki ya na bukatar amincewar majalisar dokoki cikin kwanaki biyu ko goma.
Ba tare da amincewar majalisa ba, NBA ta dage cewa ayyana dokar ta bacin da shugaban kasa ya yi ba ta da inganci kuma ba za ta yi tasiri ba.
An nemi 'yan Najeriya su kare dimokuradiyya

Asali: Twitter
NBA ta bukaci majalisar tarayyar Najeriya da ta ki yarda da duk wani yunkuri na halatta cire shugabannin da aka zaba ba bisa doka ba.
Ta kuma gargadi cewa dakatar da shugabanni ta hanyar dokar ta-baci babbar barazana ce ga dimokuradiyya, kuma hakan na iya zama abin koyi a gaba.
NBA ta bukaci kungiyoyin farar hula, bangaren shari’a, da kasashen duniya su sanya ido domin hana ci gaba da cin zarafin doka ta karfin tsiya.
A karshe, kungiyar ta ce dole ne a kare dimokuradiyyar Najeriya, kuma bai kamata a rika amfani da dokar ta-baci wajen hambarar da gwamnati ba.
PDP ta yi watsi da dokar ta bacin Rivers
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar PDP ta yi watsi da ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas, tana mai cewa matakin Bola Tinubu ya saba wa doka.
PDP ta bayyana cewa dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara tare da naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ibas ya ci karo da kundin tsarin mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng