'Ka Nesanta Kan Ka da Rivers': PDP Ta Gargaɗi 'Shugaban Riƙo' da Tinubu Ya Nada

'Ka Nesanta Kan Ka da Rivers': PDP Ta Gargaɗi 'Shugaban Riƙo' da Tinubu Ya Nada

  • Jam’iyyar PDP ta ce ayyana dokar ta-baci a Ribas take doka ne, don haka ta yi watsi da matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka
  • PDP ta ce dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ibas ya saba wa kundin tsarin mulki na dimokuradiyya
  • Jam’iyyar ta bukaci ‘yan Najeriya su tashi tsaye don kare dimokuradiyya, ta na mai cewa wannan barazana ce ga ‘yancin masu kada kuri'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam’iyyar PDP ta yi watsi da dokar ta-baci da shugaba Bola Tinubu ya ayyana a jihar Ribas, tana mai cewa hakan take doka ne.

PDP ta ce matakin dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da kuma naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) ya saba wa kundin tsarin mulkin ƙasa.

Kara karanta wannan

Dakatar da Fubara: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan 'laifin' Wike

Jam'iyyar PDP ta yi martani da Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar Ribas
Jam'iyyar PDP ta yi watsi da dokar ta baci da Tinubu ya ayyana a Ribas. Hoto: @officialABAT, @SimFubaraKSC, @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Rivers: PDP ta yi watsi da dokar ta-bacin Tinubu

Kakakin jam’iyyar, Hon. Debo Ologunagba, a sanarwar da ya fitar a shafin PDP na X, ya ce matakin Tinubu yunkuri ne na murƙushe dimokuradiyya da danniyar ‘yancin masu kada kuri’a a Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Hon. Debo Ologunagba ta ce:

“Babu wata doka da ta bai wa shugaban kasa ikon dakatar da zababben gwamna, balle kuma ayi batun naɗa wanda ba a zabe shi ba a matsayin madadinsa."

PDP ta ce wannan mataki na gwamnatin tarayya yunkuri ne na mamaye jihar Ribas, wanda APC ta jima tana ƙoƙarin aiwatarwa ta hanyar haddasa rikici.

“Tun farko, APC ta na kokarin haddasa rudani a Ribas, yanzu kuma tana son murƙushe dimokuradiyya da sunan dokar ta-baci,” a cewar PDP.

'Ba za mu yarda da kama karya ba' - PDP

Jam’iyyar ta jaddada cewa halin da ake ciki a Ribas bai cancanci a ayyana dokar ta-baci ba, don haka matakin ya saba wa kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da 'shugaban riko' na jihar Ribas, bayanai sun fito

PDP ta yi gargadin cewa wannan mataki na Tinubu wata dabara ce ta mamaye jihohi, da rage ƙarfinsu, don ƙarfafa mulkin kama karya a ƙasa.

Ologunagba ya jaddada cewa:

“Ba za mu yarda da yunƙurin kafa gwamnatin jam’iyya ɗaya a Najeriya ba. Dimokuradiyya ba mulkin kama karya ba ne."

PDP ta ce sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba shugaban kasa ikon ayyana dokar ta-baci ba tare da amincewar majalisar kasa ba.

“Kundin tsarin mulki ya bayyana cewa majalisar kasa ce ke da ikon tantance sahihancin dokar ta-baci, ba shugaban kasa kaɗai ba,”

- PDP ta jaddada.

PDP ta gargadi Ibok-Ete Ibas kan zuwa Rivers

Jam'iyyar PDP ta gargadi 'gwamnan rikon kwarya' da Tinubu ya nadawa Rivers
Shugaban PDP, Amb. Umar Damagum da wasu shugabannin jam'iyyar. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jam’iyyar ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya gaggauta janye wannan mataki, tana mai cewa hakan ka iya haddasa gagarumin rikici a ƙasar.

PDP ta ce:

“Yin watsi da kundin tsarin mulki yana iya jefa kasar nan cikin ruɗani. Dole a mutunta dokoki da ka’idojin mulkin ƙasa."

Kara karanta wannan

Rivers: Abin da manyan lauyoyi ke cewa kan matakin Tinubu na sa dokar ta baci

PDP ta kuma gargadi Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) da kada ya karɓi shugabancin jihar, tana mai cewa hakan saba wa dokar ƙasa ne.

“Ba mu ƙarƙashin mulkin soja. Babu wanda ya isa ya kafa gwamnatin kama karya a jihar Ribas,”

- in ji jam’iyyar PDP.

PDP ta bukaci jama’a da sauran jam’iyyun siyasa da su tashi tsaye don kare dimokuradiyya, domin a cewarta, wannan yunƙuri barazana ce ga ‘yancin ƙasa.

A gefe guda, bangarori da dama na siyasar Najeriya na yiwa PDP sukar kasancewar jam'iyyar adawar da ba ta da tasiri sosai a kasar.

Hakazalika, wasu na yiwa Bola Ahmad Tinubu kallon mai yiwa harkar siyasar kasar katsa-landan tare da shiga hurumin kotunan kasar.

An jibe sojoji a gidan gwamnatin jihar River

A wani labarin, mun ruwaito cewa, awanni da shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Rivers, an ga sojoji da tankokin yaki suna shawagi a fadar gwamnatin Rivers.

Kara karanta wannan

'Za a iya samun karamin yaki a Rivers,' 'Yan Neja Delta sun gargadi Tinubu

Wasu shaidun gani da ido sun ce sojoji sun mamaye gidan gwamnatin Rivers yayin da ba a san inda Gwamna Siminalayi Fubara yake ba, tun bayan dakatar da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan ta hanyar kara bayani kan matsayar jama'a kan matakin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.