Yusuf Buhari Ya Gana da Gwamna Radda bayan Sayen Fom din Takara a Katsina

Yusuf Buhari Ya Gana da Gwamna Radda bayan Sayen Fom din Takara a Katsina

  • Dan tsohon shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari ya saye fom din tsayawa takara a zaben 2027 a karkashin jam'iyyar APC mai mulki
  • Yusuf Buhari ya mika godiya ga jam'iyyar APC bisa amincewa ta ba shi damar tsayawa takara ba tare da an yi zaben fitar da gwani ba
  • Gwamnatin jihar Katsina da Gwamna Dikko Radda ke jagoranta ta yi magana game da takarar Yusuf Buhari bayan ya ziyarci fadar mulki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya gana da Yusuf Muhammadu Buhari bayan sayen fom din tsayawa takara a 2027.

Jam'iyyar APC mai mulki ta amince da Yusuf Muhammadu Buhari ya tsaya takara ya wakilci mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua a majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027

Yusuf Buhari da Dikko Radda
Lokacin da Yusuf Buhari ya ziyarci Dikko Radda a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Yusuf Buhari ya yi bayan ganawa da gwamna Dikko Umaru Radda a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Yusuf Buhari ya gana da Dikko Radda

Bayan ganawa da gwamna Dikko Umaru Radda, Yusuf Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya karbi fom din tsayawa takara a wajen shi.

Ya ce:

"A yau a Katsina, na samu damar karɓar takardun tsayawa takara a hukumance daga Mai Girma Gwamna Dikko Umar Radda.
"Ina matuƙar godiya da amincewar da aka nuna mini, kuma zan ci gaba da jajircewa wajen hulɗa da al’ummarmu tare da yin aiki tukuru domin samar da wakilci mai ma’ana."

Yusuf Buhari ya yaba wa jam'iyyar APC

Bayan jam'iyyar APC ta ba Yusuf Buhari damar tsayawa takara ba hamayya, dan tsohon shugaban kasar ya mika godiya da masu ruwa da tsaki.

Ya ce:

"Alhamdulillah, na amince da wannan takara cikin tawali’u da cikakkiyar godiya. Zan ci gaba da ƙarfafa hulɗa da jama’a tare da yin aiki tare domin samar da cigaba mai ɗorewa da amfanar kowa da kowa, in sha Allah."

Kara karanta wannan

Zance ya kare: APC ta ba Yusuf Buhari tikitin takara a jihar Katsina

Gwamna Dikko Radda da Yusuf Buhari
Yusuf Buhari, gwamna Dikko Radda da 'yan APC a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Bayanin gwamnatin jihar Katsina

Mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa Dikko Radda da manyan 'yan siyasa sun gana da Yusuf Buhari.

Ya ce:

"Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya karɓi ɗan takarar mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua, Hon. Yusuf Muhammadu Buhari, wanda ya gabatar masa da takardun takara a Fadar Gwamnati da ke Katsina."

Ya kara da cewa:

"Wadanda suka hallara sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabiru Masari; mai kula da AUDA-NEPAD na ƙasa, Hon. Jabiru Tsauri; da kuma sauran masu ruwa da tsaki daga mazabar."

Sakon Radda ga iyalan Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa ba zai ci amanar marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Ya bayyana haka ne yayin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC suka raka Yusuf Buhari gidan gwamnatin jihar Katsina a makon da ya wuce.

A wajen taron, gwamna Radda ya nuna cewa zai goyi bayan Yusuf Muhammadu Buhari ya wakilci mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng