Rivers: Abin da Manyan Lauyoyi Ke Cewa kan Matakin Tinubu na Sa Dokar Ta Baci
- Dokar ta ɓaci da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ayyana a jihar Rivers na ci gaba da haifar da cece-kuce a Najeriya a halin yanzu
- Wasu manyan lauyoyi sun tofa albarkacin bakinsu, suka soki matakin da shugaban ƙasan ya ɗauka kan rikicin siyasar Rivers
- Sun nuna kuskuren da ke cikin dakatar da zaɓaɓɓun jami'an gwamnatin jihar da shugaban ƙasan ya yi har na tsawon watanni shida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Manyan lauyoyi masu matsayin (SAN), Ebun-Olu Adegboruwa da Abeny Mohammed, sun yi magana kan dokar ta ɓacin da shugaba Bola Tinubu ya sanya a jihar Rivers.
Manyan lauyoyin sun soki matakin ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers da shugaba Bola Tinubu ya yi a ranar Talata, 19 ga watan Maris 2025.

Asali: Twitter
Lauyoyi sun soki matakin Tinubu kan rikicin Rivers
Manyan lauyoyin sun bayyana hakan ne a cikin wata hira daban-daban da suka yi da jaridar Daily Trust a daren jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyoyi sun bayyana cewa ayyana dokar ta ɓaci da kuma dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, ba bisa ka’ida ba ne kuma ba abin yarda ba ne a tsarin dimokuraɗiyya.
Biyo bayan rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar Ribas, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar mai arzikin man fetur, ya dakatar da Fubara, Odu da ƴan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Me Lauyoyi suka ce kan dakatar da Fubara?
Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) ya buƙaci shugaban ƙasa da ya janye matakin cire zaɓaɓɓun jami’an gwamnati a jihar Rivers.
Babban lauyan ya bayyana cewa dole a bi tsarin dimokuradiyya wajen magance matsalolin da ake fama da su a jihar.
"Matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka ya nuna cewa tuni ya riga ya yanke hukunci kan lamarin, kuma akwai son kai a ciki."
"Ni ba na goyon bayan ayyukan gwamnan ko ministan Abuja, amma wannan mataki ya rusa zaɓin dimokuradiyya na mutanen jihar Rivers."
"Wannan mataki da shugaban ƙasa ya dauka ba shi da tushe, ba na dimokuradiyya ba ne, kuma babu buƙatar yin hakan."
- Ebun-Olu Adegboruwa
Adegboruwa ya kuma nuna alamar tambaya kan dalilin da yasa ba a ayyana dokar ta-ɓaci a jihohin Osun da Benue ba, inda ake da matsalar rikicin ƙananan hukumomi, ko kuma a Legas, inda aka samu shugabannin majalisar jiha biyu a rana guda.
Shugaban kasa Tinubu ya tsaurara da yawa
Haka nan, Abeny Mohammed ya bayyana cewa matakin da shugaban ƙasan ya ɗauka ya yi tsauri sosai kuma ya saɓawa kundin tsarin mulki.
"Gwamnan jihar Rivers an zaɓe shi ne bisa ƙa'ida a karkashin kundin tsarin mulki, kuma ba za a iya cire shi ba sai an bi dokokin da kundin tsarin mulkin ya gindaya."
- Abeny Mohammed
Sai dai wani babban lauya, Dayo Akinlaja (SAN), ya ce lamarin ya wuce a duba shi daga fuskar shari’a kawai, yana mai cewa rikicin da ke faruwa a jihar Rivers sakamakon rikicin siyasa ne.
Gwamnonin PDP sun soki Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar PDP sun yi watsi da matakin da Bola Tinubu ya ɗauka na sanya dokar ta ɓaci a jihar Rivers.
Gwamnonin na PDP sun zargi shugaban ƙasan da nuna son kai a cikin rikicin siyasar da ke faruwa a jihar mai arziƙin mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng