'Za a iya Samun Karamin Yaki a Rivers,' 'Yan Neja Delta Sun Gargadi Tinubu

'Za a iya Samun Karamin Yaki a Rivers,' 'Yan Neja Delta Sun Gargadi Tinubu

  • Al’ummomin da ke yankunan da ake samar da mai da gas a Neja Delta sun gargaɗi cewa dokar ta-baci a Rivers na iya haddasa yaƙin sari-ka-noke
  • Wani jagora a yankin, Joseph Ambakaderimo ya ce matsalar na bukatar warwarewa ta hanyar diflomasiyya, ba kafa dokar ta-baci ba
  • Ya yi zargin cewa wasu tsofaffin ‘yan tada kayar baya da aka ware daga kwangilar sa ido kan bututun mai na iya haddasa hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Kasa da sa’o’i 24 bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Rivers, wasu 'yan yankin Neja Delta sun nuna damuwa cewa matakin ka iya haddasa yaki.

Sun bayyana cewa harin da aka kai kan babban bututun mai na Trans-Niger da ke Bodo, karamar hukumar Gokana, na iya zama sakamakon ɓacin ran tsofaffin ‘yan tada kayar baya.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hargitse ana shirin tattauna maganar dakatar da Gwamna Fubara

Fubara
An gargadi Tinubu kan sanya dokar ta baci a Rivers. Hoto: Bayo Onanuga|Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Shugaban mutanen yankin da ake samar da mai da gas a Neja Delta, Joseph Ambakaderimo, ya bukaci a sake duba matakin domin gudun tabarbarewar tattali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yiwuwar rikicin Rivers ya shafi tattali

Ambakaderimo ya yi tir da matakin shugaba Tinubu, yana mai cewa rikicin siyasar Rivers na iya zama rikicin tattalin arziki idan ba a dauki matakin diflomasiyya ba.

Ya ce ba a kai matakin da zai tilasta kafa dokar ta-baci ba, kuma hakan na iya janyo yaki a yankin Neja Delta.

Ya yi gargadin cewa wasu tsofaffin ‘yan tada kayar baya na iya amfani da wannan rikici don haddasa hare-haren da ka iya dagula harkar samar da mai da gas.

Joseph Ambakaderimo ya ce:

"Gwamnati ta sake duba kwangilar sa ido kan bututun mai don tabbatar da adalci ga kowa. Idan haka bai faru ba, yana iya shafar tattalin arzikin kasa,"

Kara karanta wannan

An gano inda Gwamna Fubara yake bayan sojoji sun mamaye fadar gwamnatin Ribas

Illar rikicin Rivers wajen samar da fetur

Ambakaderimo ya bayyana cewa a halin yanzu, daga cikin manyan matatun gas guda shida na NLNG, biyu ne kawai ke aiki, lamarin da ke haddasa raguwar samar da iskar gas a Najeriya.

Ya ce idan matsalar ta shafi samar da man fetur ma, Najeriya za ta fuskanci matsanancin koma baya a fannin tattalin arziki.

Ya bukaci gwamnatin tarayya ta tuntubi shugabannin al’ummomi domin samun maslaha ta hanyar diflomasiyya, ba daukar matakan da za su iya dagula lamarin ba.

Shugaban al'ummar ya ce:

"Idan ba a yi hattara ba, matsalar za ta dagula lamura kuma ta haddasa rikici mai muni da zai shafi tattalin arzikin kasa gaba daya,"

Kiraye-Kirayen sasanta rikicin hugar Rivers

Ambakaderimo ya bukaci Gwamna Siminalayi Fubara da ya nemi hanyar sasanci da shugaba Tinubu ta hannun manyan dattawan kasa domin a sake duba batun dokar ta-baci.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Lauyoyin Najeriya sun kawo dokokin da suka hana Tinubu dakatar da Fubara

Ya kuma caccaki ‘yan majalisar dokoki 27 na jihar da suka bijire wa hukuncin kotu, inda ya zargi su da fifita bukatun siyasa fiye da doka da oda.

"Gwamna Fubara ne kadai ke kokarin aiwatar da hukuncin kotu, amma ‘yan majalisa sun dage kan kawar da shi daga mukaminsa,"

- Joseph Ambakaderimo

Matasa sun yi rubdugu wa Shehu Sani

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani ya kare matakin shugaba Bola Tinubu na sanya dokar ta baci a Rivers.

Sai dai biyo bayan bayyana ra'ayinsa kan lamarin, matasan Najeriya sun masa rubdugu da cewa ba matakin ya kamata a dauka ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng