Rivers: Ƴan Majalisa Sun Fadi Matsayarsu kan Dokar Ta Ɓaci, Sun Fadi Mai Laifi
- Majalisar dokokin Jihar Rivers ta marabci dokar-ta-baci da Bola Tinubu ya ayyana, tana mai dora laifi kan Gwamna Simi Fubara
- Shugaban majalisar, Martin Amaewhule, ya ce Fubara ya karya dokoki da dama daga ciki akwai hana majalisa aiki yadda ya kamata
- Amaewhule ya ce matakin shugaban kasa ya na da amfani ga kasa baki daya, yana kuma kira ga jama'a su kwantar da hankalinsu
- Majalisar dokokin Ribas ta ce za ta yi aiki tare da sabon shugaban mulki domin dawo da zaman lafiya da shugabanci nagari a jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Majalisar dokokin Rivers ta yi martani bayan shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar-ta-baci a jihar.
Majalisar dokokin ta goyi bayan ayyana dokar-ta-baci da shugaba Tinubu ya yi sakamakon rikicin siyasa da ya daɗe a jihar wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Asali: Facebook
Rivers: Majalisa ta fadi ra'ayinta kan matakin Tinubu
A cewar shugaban majalisar, Martin Amaewhule, majalisar ta dora laifi kan Siminalayi Fubara bisa halayensa na danniya da tauye doka, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta nuna damuwa game da yadda Gwamna Fubara ke mulkin kama karya da danniya kamar yadda kotu ta tabbatar inda ta ce daukar matakin ya zama dole.
Sanarwar ta ce:
“Halayen danniya da take hakkin Gwamna, kamar yadda kotuna suka tabbatar, sun hana majalisar Rivers gudanar da aikinta cikin kundin tsarin mulki."
Amaewhule ya bayyana matakin shugaban kasa a matsayin abin da ya dace da muradun ƙasa, yana mai roƙon jama'a su kwantar da hankali babu abin da zai faru a jihar.
Ya ce:
“Mun yarda da wannan mataki duk da ba haka muke fata ba, amma za mu mutunta shi saboda alheri ga ƙasa.
“Shugaban kasa ya yi abin da ya dace don haka muna roƙon ku, ku kwantar da hankali yayin da sabon shugaba zai fara aiki.”

Asali: UGC
Majalisa ta ba al'ummar jihar Rivers tabbaci
Amaewhule ya tabbatar wa da al’umma cewa majalisar za ta mutunta matakin da aka ɗauka tare da goyon bayan sabon shugaba da aka naɗa.
Ya ce Majalisar Rivers na ba da cikakken goyon baya ga sabon shugaban mulki kuma za ta taimaka masa wajen dawo da zaman lafiya da shugabanci nagari.
Ayyana dokar-ta-baci ya zama wata babbar alama a rikicin siyasar Jihar Rivers da ya shafe fiye da shekara guda yana gudana.
Gwamnonin PDP sun soki matakin Tinubu a Rivers
Mun ba ku labarin cewa Gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun nuna rashin gamsuwarsu kan dakatarwar da aka yi wa Gwamna Siminalayi Fubara a Rivers.
A cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar gwamnonin na PDP, Bala Mohammed ya soki matakin da shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na dakatar da gwamnan jihar Rivers.
Gwamnan ya nuna cewa dakatarwar babbar barazana ce ga dimokuraɗiyya ƙasar nan inda ya bayyana fargaba kan matakin da aka dauka wanda ka iya zama matsala a kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng