2027: Rigima Ta Kunno Kai a ADC kan 'Tikitin' Kwankwaso/Obi da Atiku, Amaechi

2027: Rigima Ta Kunno Kai a ADC kan 'Tikitin' Kwankwaso/Obi da Atiku, Amaechi

  • Jam’iyyar ADC na fuskantar rikici kan wanda zai tsaya takarar shugaban kasa a zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara
  • Rigimar ta kunno kai ne game da takara tsakanin Peter Obi, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Rotimi Amaechi
  • Wasu jiga-jigan ADC na goyon bayan tikitin Obi da Kwankwaso, yayin da wasu ke marawa Atiku tare da Seyi Makinde ko Amaechi baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar ADC ta sake fadawa cikin wani rikici yayin da Kotun Koli ta yi hukunci kan rigimar shugabanci.

Hukuncin kotun na ranar Alhamis 30 ga watan Afrilu an 2026 ya tabbatar da damar ta na shiga zaben shugaban kasa na 2027.

Rigingimu sun taso a ADC kan tikiti Kwankwaso, Obi da Atiku da Amaechi
Jiga-jigan ADC, Atiku Abubakar, Rabi'u Kwankwaso da Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi.
Source: Facebook

Rikicin da ke damun jam'iyyar ADC

Sai dai rahoton Punch ya ce jam’iyyar na fuskantar babban kalubale wajen zaben dan takara daya daga cikin manyan ‘yan siyasa masu karfi da suka shiga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

APC ta fitar da dan takarar gwamna a Oyo, ta juyawa ministan Tinubu baya

Har yanzu ADC na fama da shari’o’i daban-daban a kotu, yayin da wasu tsofaffin mambobi ke nuna bacin rai kan yadda sababbin shiga suka mamaye jam’iyyar.

Wannan rikici ya kara bayyana matsalar son kai da gwagwarmayar iko tsakanin shugabannin jam’iyyar.

Sunayen da ake alakantawa da takarar shugaban kasa sun hada da Peter Obi, Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, Rotimi Amaechi da Mohammed Hayyatu-Deen.

Rahoton ya bayyana cewa idan zaben fitar da gwani ya rikide zuwa rikici, wadanda suka fadi za su iya ficewa daga jam’iyyar.

Hakan na iya maimaita matsalar da jam’iyyun adawa suka dade suna fuskanta a Najeriya, cewar Daily Post.

Sabuwar dokar zabe ta 2026 da jadawalin INEC sun takaita damar sauya jam’iyya bayan wa’adin mika rajistar mambobi ranar 10 ga watan Mayu.

Tikitin Kwankwaso da Obi na kara karfi a Najeriya
Jagoran Kwankwasiyya a Najeriya, Rabi'u Kwankwaso da Peter Obi. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso, Peter Obi.
Source: Twitter

Yadda magoya bayan ADC suka rarrabu

A yanzu akwai bangarori biyu a ADC, inda wasu ke marawa tikitin Obi da Kwankwaso baya saboda karfin matasa da kwarewarsu.

Wasu kuma suna goyon bayan Atiku tare da Makinde ko Amaechi saboda tasirin da suke da shi a Arewa da Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: Da gaske an kona gidan Nafiu Bala a Gombe? an samu gaskiya

Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, wanda har yanzu yana PDP, ya karbi bakuncin taron manyan jiga-jigan adawa a Ibadan.

Bayan taron, shugabannin sun yi alkawarin tsayar da dan takara guda domin kalubalantar Bola Tinubu a 2027.

Tasirin Kwankwaso, Obi da Atiku

Rahoton ya bayyana Peter Obi a matsayin wanda ke da farin jini musamman tsakanin matasa da mazauna birane.

Atiku Abubakar na da kwarewa da manyan alaka a kasa baki daya, amma yawan neman takara da batun shekaru na zama kalubale gare shi.

Kwankwaso kuwa na da karfi sosai a Kano amma tasirin sa bai gama bazuwa a kasa baki daya ba.

Ana kallon Rotimi Amaechi a matsayin gogaggen dan siyasa mai jajircewa, amma har yanzu yana bukatar karin karbuwa daga talakawa.

Wasu jiga-jigan ADC suna ganin tikitin Obi da Kwankwaso na tayar da hankalin gwamnatin APC.

Jigon ADC ya magantu kan rigimarta

Masoyin ADC, Adnan Mukhtar daga Kano ya shaidawa Legit ra'ayinsa kan rigimar jam'iyyar.

Ya ce yana da kyakkyawan fata game da makomar jam’iyyar duk da rashin tabbas da ake ciki.

Kara karanta wannan

Mark da Nafi'u Gombe: Kotun Koli ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin ADC

Ya ce:

“Duk da rikice-rikicen ADC, ita ce kaɗai jam’iyyar adawa da ke da ƙwazo wajen ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu."

Ana zargin Kwankwaso, Obi sun ware Atiku

A wani labarin, an ji cewa manyan 'yan adawa a Najeriya, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na kokarin kafa tikitin hadin gwiwa a karkashin ADC.

Majiyoyi sun ce suna shirin ne tare da jan hankalin shugabannin Arewa su mara musu baya kafin zaben fidda gwani na 2027.

Rahotanni sun nuna cewa sun gabatar da tsarin mulki na wa’adi guda domin shawo kan manyan masu ruwa da tsaki na Arewa su janye goyon bayansu ga Atiku Abubakar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.